Saraki ya bayar da gudunmuwar Janareto 2 ga jami'ar Kamaldeen a Ilorin

Saraki ya bayar da gudunmuwar Janareto 2 ga jami'ar Kamaldeen a Ilorin

Duk da shan mugunyar kaye a yayin babban zaben kasa na bana, shugaban majalisar dattawan Najeriya Abubakar Bukola Saraki, ya ci gaba da malalar dukiya wajen kyautatawa da kuma inganta jin dadin rayuwar al'umma a jihar Kwara.

Bayan kaddamar da katafaren aiki na inganta ci gaban gine-ginen hanyoyi a karamar hukumar Irepodun ta jihar Kwara, Saraki ya kuma bayar da gagarumar gudunmuwa a sabuwar jami'ar Muhammad Kamaldeen ta garin Ogidi a birnin Ilorin.

Bukola Saraki

Bukola Saraki
Source: Depositphotos

Majiyar mu ta shaida mana cewa, shugaban majalisar dattawan kasar nan ya bayar da gudunmuwar manyan Injina biyu masu samar da wutar lantarki wato Janareto ga sabuwar jami'ar dake mahaifar sa.

Kazalika shugaban majalisar dattawan kasar nan ranar Lahadi, 12 ga watan Mayu, ya kaddamar da katafare inganta ci gaban gine-ginen hanyoyi a yankin Omu-Aran da ke karamar hukumar Irepodun a jihar Kwara.

KARANTA KUMA: An yi rugu-rugu da gidan sharholiya a garin Abuja

A yayin da ya lashin takobi wajen malalar da dukiya ta kimanin Naira Miliyan dari biyar domin assassa sabuwar jami'ar da ke karkashin gudanar wa ta kungiyar Ansarul Islam Society of Nigeria, shugaban majlisar dattawa ya yi shimfidar tagomashi a cikin ta.

Domin hanzarta kafuwar ta, jaridar Leadership ta ruwaito cewa, tsohon gwamnan na jihar Kwara ya kuma fara aiwatar da ginin Asibiti a sabuwar jami'ar ta Muhammad Kamaldeen tare da wadata ta da kayan aiki.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.android&pid=solomonovlink

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Ku fa'idantu da manhajar mu ta Azumi a wannan wata mai albarka a wannan shafi:

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit

Online view pixel