NSITF: Buhari yayi na’am da matakan da Ngige ya dauka ya amince da nadin Kokori

NSITF: Buhari yayi na’am da matakan da Ngige ya dauka ya amince da nadin Kokori

Mun ji labari cewa fadar shugaban kasa sasanta barakar da ake fama da ita tsakanin Ministan kwadagon Najeriya watau Chris Ngige da kuma kungiyar NLC ta Ma'aikatan kasar a kan nadin shugabannin hukumar NSITF.

A halin yanzu sa-in-sar da ake yi tsakanin Dr. Chris Ngige da NLC ya zo karshe kamar yadda Femi Adesina, mai magana da yawun bakin shugaban kasa ya tabbatar da wannan a wani jawabi da aka fitar a Ranar 13 ga Watan Mayun 2019

Femi Adesina yake cewa shugaba Buhari ya fitar da matsaya a game da takkadamar da aka samu tsakanin Ma’aikata da Ministansa. A cewar shugaban kasar, NSITF tana karkashin gwamnatin tarayya ne ta hannun Ma’aikatar kwadago.

Shugaban kasar yace an kafa "Nigeria Social Insurance Trust Fund" ne domin ba Ma’aikata inshora, kuma an binciki badakalar da aka tafka na wawurar kudi har Naira Biliyan 48 da ma’aikata su ka tara daga hukumar tsakanin 2012-2015.

KU KARANTA: Matasa sun godewa Shugaba Buhari a kan nadin Emefiele a CBN

NSITF: Buhari yayi na’am da matakan da Ngige ya dauka ya amince da nadin Kokori

Shugaba Buhari ya ba Ngige gaskiya yayi tir da rikicin da aka yi
Source: Depositphotos

Shugaba Buhari ya nuna goyon bayan sa ga matakin da Ministan kwadago ya dauka kwanaki na rusa majalisar da za ta rika kula da wannan Ma’aikata, domin kawo gyara a NSITF, kamar yadda Hadimin shugaban kasar ya bayyana.

Buhari ya kuma gamsu da nada Austin Enejamo-Isire da Ministan kwadagon yayi ya jagoranci majalisar da za ta rika sa-ido a wannan hukuma. Bayan haka kuma za a nada wasu Darektoci da za su taya Enejamo-Isire wannan aiki.

A karshen Adesina ya kuma bayyana cewa gwamnatin tarayya ta amince da nadin Kwamared Frank Kokori, a matsayin shugaban da zai rika kula da ma’aikatar Michael Imoudu National Institute for Labour Studies ta Najeriya.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit

Mailfire view pixel