Shugaba Buhari ya karbi bakuncin gwamnan jihar Legas a fadar Villa

Shugaba Buhari ya karbi bakuncin gwamnan jihar Legas a fadar Villa

A ranar Litinin, 13 ga watan Mayun 2019, shugaban kasa Muhammadu Buhari cikin fadar Villa dake babban birnin kasar nan na tarayya ya karbi bankuncin Gwamnan jihar Legas, Akinwunmi Ambode.

Shugaba Buhari ya karbi bakuncin gwamnan jihar Legas a fadar Villa

Shugaba Buhari ya karbi bakuncin gwamnan jihar Legas a fadar Villa
Source: Twitter

Bayan shafe tsawon wa'adi guda na shekaru hudu a bisa karagar mulki, Gwamna Ambode ya yi fashin baki da cewa a halin ya kara wayo da kuma samun arziki na fahimtar yadda siyasa ta ke a kasar nan.

Ambode ya bayyana hakan yayin ziyarar da ya kai wa shugaban kasa Buhari. Ya ce ziyarar sa ta kasance domin bayyana murna da kuma mika godiya ta musamman ga jagoran kasar.

Shugaban kasa Buhari a watan da ya gabata cikin birnin Legas, ya kaddamar da wasu muhimman ayyuka na inganta ci gaba da bunkasar jin dadin rayuwar al'umma da babu makamancin su a duk fadin Najeriya.

KARANTA KUMA: Domin na kasance jakadan zaman lafiya ya sanya zan hakura da kujerar Sanata - David Mark

Ko shakka babu gwamna Ambode ya yi rashin sa'a ta shan mugunyar kaye yayin zaben fidda gwanin takarar kujerar gwamnan jihar Legas a karkashin inuwa ta jam'iyyar APC.

Sai dai a yayin ya kasance dabi'a da kuma al'ada ta rayuwa, gwamna Ambode a kullum idanuwan sa na kara budewa ta fuskar samun arziki na fahimtar yadda al'amurran siyasa ke gudana a kasar nan.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.android&pid=solomonovlink

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Ku fa'idantu da manhajar mu ta Azumi a wannan wata mai albarka a wannan shafi:

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit

Mailfire view pixel