Ba wani liyafar azo a gani za a yi ba a ranar rantsar da Buhari – Gwamnatin tarayya

Ba wani liyafar azo a gani za a yi ba a ranar rantsar da Buhari – Gwamnatin tarayya

Bikin rantsar da Shugaban kasa Muhammadu Buhari a karo na biyu da za a yi a ranar 29 ga watan Mayu, 2019, ba zai kasance wani babban liyafa ba, inji ministan labarai da al’adu, Lai Mohammed.

Mista Mohammed wanda yayi jawabi ga manema labarai a fadar Shugaban kasa a ranar Litinin, 13 ga watan Mayu, yace wasu bukukuwa da aka shirya a yayin bikin rantsarwar za su gudaana ne a ranar bikin June 12 na farko da za a yi a matsayin ranar damokradiyyar Najeriya.

Ministan yace an yanke hukuncin yin bikin rantsarwar cikin sauki ne a taron majalisar zartarwa wanda ya gudana a ranar Laraba, 8 ga watan Mayu.

Ba wani liyafar azo a gani za a yi ba a ranar rantsar da Buhari – Gwamnatin tarayya

Ba wani liyafar azo a gani za a yi ba a ranar rantsar da Buhari – Gwamnatin tarayya
Source: Facebook

Yace, sai dai an tura wasikar gayyata ga dukkanin shugabannin duniya domin su halarci bukukuwan da aka shirya don bikin ranar Damokradiya a ranar 12 ga watan Yuni.

KU KARANTA KUMA: Tarin motocin alfarma: Me zaka fada ma Allah – Gudaji Kazaure ya tambayi Dino Melaye

Ya kuma bayyana cewa kasar baa za ta iya gudanar da manyan bukukuwa biyu cikin tazarar mako biyu ba.

Yace za a sanar da cikakken bayanin bukukuwan da aka shirya domin wadannan ranaku a taron labarai na duniya wanda aka shirya yi a ranar 20 ga watan Mayu a Abuja.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Ku fa'idantu da manhajar mu ta Azumi a wannan wata mai albarka a wannan shafi: https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit

Mailfire view pixel