Farfesa Osinbajo ya bude wasu kamfanonin sarrafa mai da sabulai a jahar Bauchi

Farfesa Osinbajo ya bude wasu kamfanonin sarrafa mai da sabulai a jahar Bauchi

Mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo ya bayyana cewa babban abinda gwamnatin APC ta shugaban kasa Buhari ta sanya a gaba shine kula da walwalar dan Najeriya, kuma akan haka zata cigaba da gudanar da mulki bayan rantsar da ita a ranar 29 ga watan Mayu.

Legit.ng ta ruwaito Osinbajo ya bayyana haka ne yayin da yake kaddamar da fara aikin wasu manyan kamfanoni guda biyu na sarrafa man gyada da sabulai a jahar Bauchi yayin ziyarar aiki na yini guda daya kai jahar.

Farfesa Osinbajo ya bude wasu kamfanonin sarrafa mai da sabulai a jahar Bauchi
Farfesa Osinbajo
Source: UGC

KU KARANTA: Tarin motocin alfarma: Me zaka fada ma Allah – Gudaji Kazaure ya tambayi Dino Melaye

Haka zalika Osinbajo ya kaddamar da ofishin hukumar tsarin kiwon lafiya ta jahar da kuma gidauniyar kiwon lafiya ta jahar Bauchi, bugu da kari mataimakin shugaban na Najeriya ya kaddamar da wani aikin samar da wutar lantarki da gwamnatin jahar Bauchi tayi a kauyen Burra dake karamar hukumar Ningi.

Farfesa Osinbajo ya bude wasu kamfanonin sarrafa mai da sabulai a jahar Bauchi
Osinbajo
Source: UGC

Osinbao yace kirkirar hukumomin kula da kiwon lafiya da Gwamna M.A Abubakar yayi zai taimaka ma gwamnatin tarayya wajen cimma manufofin da ta sanya a gaba na samar da ingataccen kiwon lafiya ga yan Najeriya.

Ya kara da cewa “Babban abinda shugaba Buhari yasa a gaba shine kyautata ma yan Najeriya, don haka ne ya kirkiro da sabbin tsare tsaren tallafi kamarsu N-Power, ciyar da daliban Firamari, Trader Moni da ire irensu don rage ma yan Najeriya radadin talauci.”

Shima a nasa jawabin, Gwamna Abubakar ya bayyana cewa sun kirkiro tsare tsaren kiwon lafiyan ne domin cike gibin da ake samu wajen samun ingantaccen kiwon lafiya a jahar, ya kara da cewa sun tara kudin gudanar da tsare tsare ne ta yankan wani kaso daga kudaden harajin jahar, harajin kwangila, kudaden kananan hukumomi da sauransu.

Farfesa Osinbajo ya bude wasu kamfanonin sarrafa mai da sabulai a jahar Bauchi
Farfesa Osinbajo a jahar Bauchi
Source: Facebook

Daga karshe a yayin ziyarar tasa, Osinbajo ya ziyarci guda daga cikin masu kanana masana'antu a jahar Bauchi, Muhammad Musa Usman har gida, inda ya zanta dashi akan kalubalen da suke fuskanta, har mayayi hoto da iyalan mutumin.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Online view pixel