Yanzu Yanzu: Kungiyar NLC ta fara zanga-zangar game-gari

Yanzu Yanzu: Kungiyar NLC ta fara zanga-zangar game-gari

Kungiyar kwadago na Najeriya (NLC) ta fara zanga-zangar game-gari akan rikicin shugabanci a Hukumar Gudanarwar NSITF.

Zanga-zangar game-garin, wanda aka fara da karfe 9am na ranar Litinin, 13 ga watan Mayu ya fara ne daga heakwatar hukumar kwadago da ke babbar birnin tarayya Abuja.

Daga NLC har Ma’aikatar Kwadago na goyon bayan wani bangare daban na Shugaban hukumar ta NSITF.

Jiya Lahadi, 12 gaq watan Mayu kungiyar ta ce yanke hukuncin fara yajin aikin ya zama tilas, saboda matakin da Ministan Kwadago, Chris Ngige ya dauka na da goyon baya da kuma sa hannun Shugaba Muhammdu Buhari.

Ta ce za a rantsar da hukumar gudamarwar NSITF a yau Litnin a babbar birnin tarayya, Abuja. Shi ya sa su kuma za su tsunduma yajin aki.

Yanzu Yanzu: Kungiyar NLC ta fara zanga-zangar game-gari

Yanzu Yanzu: Kungiyar NLC ta fara zanga-zangar game-gari
Source: Twitter

NLC ta ce su na mmakin yadda za a tura Frank Kokori ya tafi Cibiyar Horas da Ma’aikatan Kwadago a Ilorin, bayan daga farko shi ne aka tura shugabancin Hukumar Gudanarwar NISTF.

KU KARANTA KUMA: Ba za a taba samun zaman lafiya ba a Najeriya har sai dan Igbo ya zama Shugaban kasa - Nwobodo

Kungiyar dai ta na goyon bayan Frank Kokori, yayin da a daya gefen kuma ta na zargin Minista Ngige ne ba ya goyon bayan sa, shi ya sa ya ki amincewa da nadin da aka yi masa tun da farko.

Shugaban NLC Ayuba Wabba ya shaida dalilin da ya sa suke zanga-zangar, kuma ya ce za a yi zanga-zanga a Majalisar Dinkin Duniya a ofishin da ke Genewa a ranar 18 ga watan Mayu.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Ku fa'idantu da manhajar mu ta Azumi a wannan wata mai albarka a wannan shafi: https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit

Tags:
Online view pixel