Abinda yasa Ganduje bai tsige sarki Sanusi II ba

Abinda yasa Ganduje bai tsige sarki Sanusi II ba

Wata majiyar gwamnatin Kano ta bayyana yadda gwamnan jihar, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya so ya tsige sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II, ba don Alhaji Aliko Dangote ya gaggauta shiga tsakani ba.

Majiyar da ta nemi a boye sunanta, ta ce sarki Sanusi II ne da kan sa ya roki Dangote a kan ya lallashi Ganduje ya fasa cire shi daga kujerar sarkin Kano bayan ya fuskanci dangantakar dake tsakanin fada da gwamnati ta lalace sosai.

"Ana fara maganar sake bude binciken zargin badakala da kudin masarauta da kuma batun kirkirar karin sabbin sarakuna, sarkin ya aiko hamshakin dan kasuwa, Alhaji Aliko Dangote wurin Ganduje domin ya roke shi a kan ya fasa cire shi daga kujerar sarkin Kano.

"Amma sai Ganduje ya shaida wa Dangote cewar ya koma ya sanar da Sanusi II cewar yana da zabi guda uku; ko ya yi murabus da kan sa ko gwmnati ta tsige shi ko kuma ta kirkiri karin sabbin masarautu hudu a jihar.

Abinda yasa Ganduje bai tsige sarki Sanusi II ba
Ganduje da sarki Sanusi II
Source: Facebook

"Ganduje ya bawa Dangote tabbacin cewar dole gwamnatin jihar Kano za ta kaddamar da daya daga cikin zabin guda uku tunda sarki Sanusi II ba zai daina shiga harkokin nuna adawa da shi a siyasance ba. Ba don Dangote ya shiga tsakani ba, babu abinda zai hana Ganduje ya tube Sanusi," a cewar majiyar.

DUBA WANNAN: Gwamnan CBN ya ziyarci Buhari (Hotuna)

Majiyar ta kara da cewa, duk da hakan ba lallai gwamna Ganduje ya hakura ba gaba daya, akwai yiwuwar ya canja shi zuwa daya daga cikin sabbin masarautu hudu da aka kirkira, sannan ya maye gurbin sa da daya daga cikin sabbin sarakunan da aka nada ranar Asabar.

Daga cikin gyaran dokar masarautu da majalisar dokokin jihar Kano tayi, akwai batun yin canji a tsakanin sarakuna zuwa kowacce daga cikin masarautu biyar da yanzu Kano keda su. Duk wanda ya gaji sarautar Kano, ta iyaye ko kakanni, zai iya zama sarkin kwaryar birnin Kano.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.android&pid=solomonovlink

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel