Yanzu Yanzu: Zainab Aliyu ta iso gida Najeriya daga kasar Saudiyya, hotuna

Yanzu Yanzu: Zainab Aliyu ta iso gida Najeriya daga kasar Saudiyya, hotuna

Zainab Aliyu ta iso gida Najeriya bayan gwamnatin kasar Saudiyya ta sake ta, jaridar Daily Independent ta bayyana hakan a ranar Litinin, 13 ga watan Mayu.

Ku tuna cewa an kama dalibar yar Najeriya a kasar Saudiyya bisa zargin safarar miyagun kwayoyi sannan daga bisani aka sake ta bayan gwamnatin Najeriya ta sanya baki a lamarin.

Zainab dai ta dawo gida ne a yau Litinin, 13 ga watan Mayu da misalin karfe 10 na safe.

Jirgi ya sauke ta a Kano inda ta tarar da dandazon yan uwa da abokan arziki suna jira domin tarbarta.

Yanzu Yanzu: Zainab Aliyu ta iso gida Najeriya daga kasar Saudiyya, hotuna

Zainab Aliyu ta samu tarba daga yan uwa da abokan arziki a lokacin da ta iso kasar
Source: Facebook

A baya Legit.ng ta rahoto cewa, Hukumomin kasar Saudiyya sun kama Zainab, daliba a jami'ar Maitama Sule dake Kano, a ranar 26 ga watan Disamba na shekarar 2018 bisa zarginta da shiga da jaka dauke da kwayar 'tramol' zuwa kasar Saudiyya.

KU KARANTA KUMA: Alhamdulillahi: Anyi mani aiki cikin nasara kuma ina samun lafiya – Tsohuwar ministar Buhari

Matashiyar ta tashi zuwa kasar Sauddiya daga filin jirgin sama na Mallam Aminu domin gudanar da aikin 'umra' tare da mahaifiyarta, Maryam, da 'yar uwarta, Hajara.

Babbar mai taimaka wa shugaban kasa a bangaren harkokin da suka shafi kasashen waje, Abike Dabiri Erewa, ce ta sanar da umarni da shugaba Buhari ya bayar a ranar Litinin, 29 ga watan Afrilu, ta kara da cewa tuni gwamnatin tarayya ta fara tattauna batun sakin Zainab tare da wasu mutane biyu dake da irin matsalar da Zainab ta samu.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Ku fa'idantu da manhajar mu ta Azumi a wannan wata mai albarka a wannan shafi: https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel