Alhamdulillahi: Anyi mani aiki cikin nasara kuma ina samun lafiya – Tsohuwar ministar Buhari

Alhamdulillahi: Anyi mani aiki cikin nasara kuma ina samun lafiya – Tsohuwar ministar Buhari

Tsohuwar ministar da ke kula da harkokin mata, Hajiya Aisha Jummai Alhassan ta nuna farin ciki da godiya ga dukkanin yan Najeriya da suka nuna kulawarsu da addu’o’i a gareta a lokacin da take fama da rashin lafiya.

Aisha ta bayyana a shafinta na Facebook cewa anyi mata aiki cikin nasara, kuma sannan ta ci gaba da samun sauki a kullun.

Ta kuma yi hamdala ga Allah madaukakin sarki da Ya tashi kafadarta lafiya.

Alhamdulillahi: Anyi mani aiki cikin nasara kuma ina samun lafiya – Tsohuwar ministar Buhari

Alhamdulillahi: Anyi mani aiki cikin nasara kuma ina samun lafiya – Tsohuwar ministar Buhari
Source: Facebook

Ta rubuta a shafin nata: "Alhamdulillah! Alhamdulillah!! Alhamdulillah!!!

“Anyi mun aiki cikin nasara kuma ina samun sauki a kullun. Nagode gare ku kan addu’o’inku, yan uwa , abokan arzki da dukkanin yan Najeriya da suka nuna kulawa. Nagode sosai sosai. Miyetti.Jazakallah Khairan.”

Alhamdulillahi: Anyi mani aiki cikin nasara kuma ina samun lafiya – Tsohuwar ministar Buhari

Alhamdulillahi: Anyi mani aiki cikin nasara kuma ina samun lafiya – Tsohuwar ministar Buhari
Source: Facebook

A baya Legit.ng ta raoto cewa, Tsohuwar ministar Buhari kuma tsohuwar 'yar takarar gwamna a jihar Taraba, Aisha Jummai Alhassan, wacce aka fi sani da 'Mama Taraba", ta nemi addu'ar jama'a a kan tiyatar canjin murfin kokon gwuiwa da za a yi mata.

KU KARANTA KUMA: Garambawul: Majalisar dokoki ta gaza wa yan Najeriya – Sanata Adeyeye

A wani sako da ta fitar a shafinta na dandalin sada zumunta (Twitter), Mama Taraba ta ce an kammala shiri tsaf domin shiga da ita dakin tiyata a asibiti, a saboda haka ta ke neman addu'a.

Mama Taraba ta ajiye mukaminta na ministar harkokin mata a gwamnatin Buhari tare da fita daga jam'iyyar APC a ranar 27 ga watan Yuli na shekarar 2018.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Ku fa'idantu da manhajar mu ta Azumi a wannan wata mai albarka a wannan shafi: https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit

Mailfire view pixel