N50: Daliban Najeriya sun umarci JAMB ta maidawa mutane kudinsu

N50: Daliban Najeriya sun umarci JAMB ta maidawa mutane kudinsu

Kungiyar NANS ta ‘Daliban Najeriya, ta zargi hukumar da ke gudanar da jarrabawar shiga makaratun gaba da jami’a watau JAMB da lashe kudin Bayin Allah da sunan aiko masu sakamakon jarrabawarsu.

NANS ta nemi hukumar JAMB ta dawowa wadanda su ka rubuta jarrabawar UTME a bana kudin da su ka kashe wajen duba jarrabawar su. An karbi N50 ta waya a wajen duk wanda ke son samun sakamakon jarrabawar da ya rubuta.

Shugaban majalisar kungiyar NANS, Kwamared Abdulmajeed Oladimeji Oyeniyi, ya nemi JAMB ta maidowa kowa wannan kudi da aka zare masa a karshen makon nan. Oladimeji Oyeniyi yayi wannan magana ne a madadin NANS.

Babban jami’in kungiyar ‘Daliban, a jawabin sa, yace babu dalilin karbar kudin mutane kafin a bayyana masu sakamakon jarrabawar UTME din na su na bana domin kuwa hukumar za ta iya turawa ‘Daliban na ta jarrabawar su kai-tsaye.

KU KARANTA: Shugaba Buhari ya ba wata Budurwa babban mukami a Najeriya

N50: Daliban Najeriya sun umarci JAMB ta maidawa mutane kudinsu

Shugaban hukumar JAMB na Najeriya, Is-Haq Oloyode
Source: UGC

Abdulmajeed Oladimeji Oyeniyi, a bakacin NANS, yace sun ba hukumar jarrabawar sa’a 48 watau kwana 2 rak da su maidawa kowa kudinsa ko kuma su gamu da fushin ‘Yan Najeriya daga kowane kwararo da sako na kasar kwanan nan.

Oyeniyi ya kara da cewa NANS ta cire-rai daga shugabancin hukumar JAMB a halin yanzu, ganin irin matakan da ta ke ta dauka. A jawabin ‘Daliban kasar sun ce ya kamata ace JAMB ta shirya tsarin CBT kafin ta soma amfani da shi.

An samu bacin lokaci a wajen jarrabawar bana inda aka yi kusan wata guda ba a fitar da sakamakon jarrabawar da aka yi ba inji kungiyar. Dimeji Oyeniyi yace wannan abin kunya ne ga Najeriya gaba daya.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit

Mailfire view pixel