Rundunar soji ta ceto mata 29 da yara 25 daga yan ta’addan Boko Haram a Borno, hotuna

Rundunar soji ta ceto mata 29 da yara 25 daga yan ta’addan Boko Haram a Borno, hotuna

Dakarun sojojin Operation Lafiya Dole tare da hadin gwiwar jami’an tsaro na sa kai na ci gaba da aikin kakkaka domin halaka yan ta’addan Boko Haram.

A haka, a ranar 11 ga watan Mayu rundunar sun yi nasarar kakkabe kauyukan Ma'allasuwa da Yaga – Munye a jihar Borno.

Ba a yi wata arangama da yan ta’addan Boko Haram ba domin sun tsere kafin isowar dakarun sojin inda suka bar wasu mutane 54 da ake zaton sun yi garkuwa dasun ne.

Daga cikin mutanen da aka ceto 29 sun kasance mata yayinda 25 suka kasance kananan yara. An kuma yi nasarar ceto dukkansu.

KU KARANTA KUMA: Garambawul: Majalisar dokoki ta gaza wa yan Najeriya – Sanata Adeyeye

Hakazalika, a kauyukan Zari-Kasake da Jumachere da ke yakin Damasak na karamar hukumar Mobbar da ke jihar Borno, sojojin Bataliya 145 na Operation Lafiya Dole sun gano sannan suka lalata motocin da ke kaiwa yan Boko Haram kayayyaki guda biyu.

Bugu a kari, an kama wani dan sandan Mopol Sergeant Markus John – mai lamba - PNo 383106 a tashar bincike na Njimtilo da ke hanyar Maiduguri- Damaturu dauke da mujalla biyu, alburusai 146 da kuma bindiga daya a jakarsa a hanyarsa ta zuwa jihar Lagas.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Ku fa'idantu da manhajar mu ta Azumi a wannan wata mai albarka a wannan shafi: https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit.ng

Online view pixel