Garambawul: Majalisar dokoki ta gaza wa yan Najeriya – Sanata Adeyeye

Garambawul: Majalisar dokoki ta gaza wa yan Najeriya – Sanata Adeyeye

- Sanata Olusola Adeyeye ya ga laifin majalisar dokokin kasar wajen gaza magance lamarin sake fasalin lamura

- Sanatan mai wakiltan Osun ta tsakiya a majalisar dokokin kasar, yace abune da ke son goyon bayan masu rinjaye

- Ya yi korafin cewa lamarin gaza isar da batun sauya fasalin lamuran kasar ya rage martabar majalisar dokokin kasar na takwas

Sanata mai wakiltan yankin Osun ta tsakiya a majalisar dokokin kasar, Sanata Olusola Adeyeye, ya ga laifin majalisar wajen gaza magance matsalar sake fasalin lamuran kasar.

Da ya bayyana a shirin Channels TV na Sunday Politics, dan majalisan yayi korafi akan cewa majalisar dokokin kasar ta takwas mai shirin barin gado ta gaza goyon bayan kai kasar ga tafarkin gaskiya.

Adeyeye, wanda ya kasance bulaliyar majalisar dokokin kasar, yayi bayanin cewa ba lallai ne yan majalisar na da kudirin kira ga sake fasalin kasar ba, sai dai ya kasance kira na mafi rinjayen yan majalisar.

Garambawul: Majalisar dokoki ta gaza wa yan Najeriya – Sanata Adeyeye

Garambawul: Majalisar dokoki ta gaza wa yan Najeriya – Sanata Adeyeye
Source: UGC

Ya tuna da wani lamari da ya taba faruwa a majalisar dokoki na bakwai inda aka gabatar da lamarin sauya kasa daga kasancewa dan Najeriya a gaban majalisar.

KU KARANTA KUMA: Malabu: Ba ni da gida ko asusun ajiya a kasar waje - Jonathan

A cewarsa, mafi akasarin yan majalisa sun yi adawa ya barin shekara 18 a matsayin minzalin balaga kamar yadda adddinin Islama ta bayyana kowani mutum mai aure a matsayin balagagge.

Yace hakkin sake kundin tsarin mulki ya rataya ne akan wuyan majalisa sai dai a kowace kasa, gyara kundin tsarin mulki baya taba zama mikakken lamari ko abu mai sauki.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Ku fa'idantu da manhajar mu ta Azumi a wannan wata mai albarka a wannan shafi: https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit

Tags:
Online view pixel