CBN: Buhari yayi daidai da ka zabi Godwin Emefiele – inji PLAN

CBN: Buhari yayi daidai da ka zabi Godwin Emefiele – inji PLAN

Wata kungiya da ake kira “The Partners for Legislative Agenda for Nigeria” (watau PLAN), ta tofa albarkacin bakinta a game da matakin da shugaban kasa ya dauka wajen nadin gwamnan CBN.

Idan ba ku manta ba a makon da ya wuce ne shugaba Muhammadu Buhari ya zabi gwamnan babban bankin Najeriya na CBN ya cigaba da rike kujerarsa. Buhari ya nemi Majalisa ta sake ba Godwin Emefiele wani wa’adin.

Wannan kungiya ta Matasan kasar nan ta ji dadin wannan zabi da shugaban kasar yayi inda tace hakan yayi mata kyau. Kungiyar tace hakan ya nuna cewa shugaba Buhari yana yi wadanda su kayi kokari a ofis sakayyan kirki.

KU KARANTA: Wata Kungiya ta ji dadin barin Emefiele a babban bankin Najeriya

CBN: Buhari yayi daidai da ka zabi Godwin Emefiele – inji PLAN

Kungiyoyi sun yabawa Buhari a kan zabin Gwamnan CBN
Source: Depositphotos

A jawabin kungiyar ta bakin Jagoranta, Khalifa Bello Adamu, wannan abu da shugaban kasa Buhari yayi yana cikin matakai masu kyau da ya dauka tun da ya hau kan mulki. Kungiyar ta PLAN tace Najeriya ta bude sabon babi.

Daily Trust ta rahoto cewa, Mallam Khalifa Bello Adamu yace Buhari ya nuna cewa yana yi wa kwazo da himma sakayya a gwamnatinsa. Kungiyar tace tana tare da Godwin Emefiele ne saboda irin namijin kokarin da yake yi.

PLAN tace gwamnan bankin yana bakin kokarinsa na farfado da tattalin arzikin Najeriya. Bello Adamu yace babu nuna banbancin siyasa wajen kwazon da gwamnan na CBN yake yi, wanda yanzu ake so a karawa shekara 5 a ofis.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit Newspaper

Mailfire view pixel