Malabu: Ba ni da gida ko asusun ajiya a kasar waje - Jonathan

Malabu: Ba ni da gida ko asusun ajiya a kasar waje - Jonathan

Tsohon Shugaban kasa, Dr Goodluck Ebele Jonathan ya bayyana cewa ba shi da wani asusun ajiya ko gida ko kuma wani kasuwanci a kasashen waje.

Jonathan na martani ne ga sabon zargin da lauyoyin gwamnatin tarayya suke mashi a wata kara da suka shigar a wata kotu da ke birnin Landan kan cinikin rijiyar mai na bogi da aka fi sani da cinikin Malabu.

Gwamnatin tarayya dai na zargin tsohon Shugaban kasar da karbar rashawa a cinikin bogin da ya gudana a baya.

Jonathan ya bayyana hakan ne a wata sanarwa daga hadiminsa, Ikechukwu Eze a ranar Lahadi, 12 ga watan Mayu.

Ya kalubalanci wadanda ke zargin nasa da su gabatar da hujja a kotu kan haka.

Malabu: Ba ni da gida ko asusun ajiya a kasar waje - Jonathan

Malabu: Ba ni da gida ko asusun ajiya a kasar waje - Jonathan
Source: UGC

A karar da gwamnatin ta shigar, ta bayyana cewa wannan cinikayyar ba a yi ta kan ka'ida ba kuma an tsara ta ne bisa son rai.

KU KARANTA KUMA: Ya kamata Sultan da sauran jama’a su nuna adawa da Ganduje – Umar Ardo

Gwamnatin dai ta nemi manyan kamfanonin mai na Eni da Shell da su biya ta diyyar dala biliyan 3.5 sakamakon bata mata suna.

Batun cinikin malabu ya jawo ce-ce-ku-ce a Najeriya a can baya ganin cewa rijiyar man da aka yi cinikinta na daya daga cikin manyan rijiyoyin mai mafi daraja a Afirka.

Ya kuma jadadda cewa imma a lokacin da yake kan kujerar mulki ko bayan barinsa mulki, maganar it ace dai cewa tsohon Shugaban kasa Jonathan “bai mallaki kowani asusun banki, kasuwanci ko kadarori a wajen Najeriya ba.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Ku fa'idantu da manhajar mu ta Azumi a wannan wata mai albarka a wannan shafi: https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit.ng News

Mailfire view pixel