Ya kamata Sultan da sauran jama’a su nuna adawa da Ganduje – Umar Ardo

Ya kamata Sultan da sauran jama’a su nuna adawa da Ganduje – Umar Ardo

Masanin tarihi kuma tsohon malamin jami’a, Dr. Umar Ardo, yayi kira ga Sultan da al’umman Musulmi da su yi adawa da kafa sabbin masarautu da Gwamna Abdullahi Ganduje na jihar Kano yayi.

Yace yunkurin zai lalata masarautar sannan ya zargi gidan sarauta da taimakawa gwamnan wajen aikata laifin.

A wata hira a karshen mako, Ardo yace: “ba wai Allah wadai kawai Sultan da dukka mambobin masarautar, al’umman Musulmi da mutanen Fulbe za su yi ba, kamata yayi su nuna tirjiya akan haka.

Ya kamata Sultan da sauran jama’a su nuna adawa da Ganduje – Umar Ardo

Ya kamata Sultan da sauran jama’a su nuna adawa da Ganduje – Umar Ardo
Source: UGC

“An rigada an kafa masarautar tun a lokacin Shehu Uthman Dan Fodio. Sannan idan ka fara rarraba su a yanzu, kawai kana rage darajar tsarin masarautar ne. Wanda ya samar da masarautar ne da asara."

Yace gwamnan na kawo rabuwar kai ne a gidan masarautar tsakanin Muhammad Sanusi II, Sarkin Kano da yan uwansa ta yadda za a dagula masarautar da al’addun gado.

KU KARANTA KUMA: Buhari ya yi ma wata kyakkyawar budurwa mai shekaru 27 nadin mukami mai muhimmanci

Yace koda dai wannan ba shine karo na farko da ake kaiwa masarautar hari ba, yin shiru zai kara karfafa masu kawo rabuwar.

A hiran, Ardo yace Sanusi bai yi laifin komai ba amma fadar gaskiya yasa aka yi masa haka.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Ku fa'idantu da manhajar mu ta Azumi a wannan wata mai albarka a wannan shafi: https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit Newspaper

Mailfire view pixel