Ta leko ta koma: Hukumar INEC ta kwace shaidar samun nasara daga zababben Sanatan PDP

Ta leko ta koma: Hukumar INEC ta kwace shaidar samun nasara daga zababben Sanatan PDP

Hukumar zabe mai zaman kanta, INEC ta janye takardar shaidar samun nasarar lashe zaben Sanata da ta baiwa zababben Sanatan jam’iyyar PDP mai wakiltar mazabar Delta ta Arewa, Sanata Peter Nwaboashi.

Legit.ng ta ruwaito darakatan sharia na hukumar INEC, Oluwatoyin Babalola ce ta bayyana haka a ranar Juma’a, 10 ga watan Mayu yayin da take mika takardar shaidar samun nasara ga abokin hamayyar Sanata Peter, watau Nd Munir Nwoko, a matsayin halastaccen zababben Sanatan Delta ta Arewa.

KU KARANTA: Yansanda sun sun ceto mutane 2 daga hannun masu garkuwa, sun kama miyagu 3

Ta leko ta koma: Hukumar INEC ta kwace shaidar samun nasara daga zababben Sanatan PDP

Munir
Source: UGC

A watan daya gabata ne wata babbar kotun tarayya dake babban birnin Abuja ta yanke hukuncin soke zaben Sanata Peter Nwaboashi, inda ta sanar da Ned Nwoko a matsain halastaccen dan takarar jam’iyyar PDP daya lashe sahihin zaben fidda gwani na jam’iyyar.

Da yake hukunci, Alkalin kotun, mai sharia A.R Mohammed ya bayyana cewa “Duba da dukkanin hujjojin da aka zube a gaban kotu, kotu ta gamsu Ned Nwoko ne ya samu nasarar lashe zaben fidda gwani na jam’iyyar PDP daya gudana a ranar 2 ga watan Oktoban 2018.”

Da wannan hukuncin kotu ne hukumar INEC ta janye shaidar samun nasarar data baiwa Sanata Peter, inda ta mikashi ga Ned Munir Nwoko, fitaccen lauya, kuma wanda ya fito daga cikin tsiraran kabilu Musulmai yan asalin jahar Delta.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Online view pixel