Yansanda sun ceto mutane 2 daga hannun masu garkuwa, sun kama miyagu 3

Yansanda sun ceto mutane 2 daga hannun masu garkuwa, sun kama miyagu 3

Jami’an rundunar Yansandan Najeriya dake aikin Operation Puff Adder sun samu nasarar cafke wasu miyagun barayin mutane uku dake satar mutane da nufin karbar kudin fansa daga iyalansa, tare da kubutar da mutane biyu da suka yi garkuwa dasu.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito kaakakin Yansanda, Frank Mba ne ya bayyana haka a ranar Lahadi, 12 ga watan Mayu a babban birnin tarayya Abuja, inda yace sun kwato bindigu guda biyu kirar AK 47 da alburusai da dama.

KU KARANTA: Yaki da rashawa: Zan iya bankado ma Buhari naira Tiriliyan 3 – Inji Abdulrashid Maina

Yansanda sun sun ceto mutane 2 daga hannun masu garkuwa, sun kama miyagu 3
Yansanda
Source: Facebook

Mba ya bayyana sunayen mutanen da suka kubutar kamar haka; Ali Abu Sale mai shekaru 34 da Bala Bawa mai shekaru 37, wadanda yace yan bindigan sun sacesu ne daga kauyen Maijaki dake karamar hukumar Lapai na jahar Neja a ranar 1 ga watan Mayu.

A cewar Mba, sun ceto Sale ne daga dajin Mai Lamba dake kusa da garin Lapai, yayin da suka ceto Bawa a kauyen Gada Biyu dake wajen garin Abuja, “kafin nan barayin sun nemi a biyasu naira miliyan 8 a matsayin kudin fansa.” Inji shi.

Haka zalika kaakakin ya bayyana sunayen miyagub masu garkuwa da mutanen kamar haka; Mohammed Bello inkiya Dan Hajiya mai shekaru 42, Suleiman Musa inkiya Dan Auta mai shekaru 38, da kuma Abubakar Bello inkiya Abu Kango mai shekaru 28, sai kuma wani guda daya mutu a musayar wuta.

Daga karshe yace barayin suna hannu a yanzu haka, kuma suna bayar da bayanai ga Yansanda bisa binciken da rundunar ta kaddamar akansu, sa’annan yace babban sufetan Yansandan Najeriya ya jinjina ma Yansandan da suka samu wannan nasara.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Online view pixel