Yaki da rashawa: Zan iya bankado ma Buhari naira Tiriliyan 3 – Inji Abdulrashid Maina

Yaki da rashawa: Zan iya bankado ma Buhari naira Tiriliyan 3 – Inji Abdulrashid Maina

Tsohon shugaban kwamitin biniciken kudin fansho da tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ya kafa, Abdulrashid Maina ya zargi shugabancin hukumar EFCC na da dana yanzu da laifin wawure naira Tiriliyan 1.63 da gidaje 222 daya kwato.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito Maina ya bayyana haka ne cikin wani hira da yayi da Ordinary Ahmed Isa a shirin Brekete Family na gidan rediyon Human Right dake Abuja, inda yace wannan ne dalilin da yasa EFCC ta matsa masa lamba, take naman wulakantashi.

KU KARANTA: Yadda wani ya aikata ma Fulani danyen aiki yayi awon gaba da garken shanunsu duka

Yaki da rashawa: Zan iya bankado ma Buhari naira Tiriliyan daya – Inji Abdulrashid Maina

Abdulrashid Maina
Source: UGC

Maina ya zargi Ibrahim Magu da magabacinsa Ibrahim Lamorde da kwashe kudaden tare da raba gidajen tsakanin wasu manyan mutane, don haka ba zasu iya bada cikakken bayanin gaskiya game da kudaden ba, ya cigaba da cewa ko a mulkin Buharin nan ma sai daya bankado wasu naira Tiriliyan 1.3 da aka sace.

Ya kuma kara da cewa ko a yanzu zai iya taimaka ma gwamnatin Buhari wajen bankado kimanin naira Tiriliyan 3 da aka sace tare da maido ma gwamnati dasu, amma wasu shafaffu da mai kuma yan gaban goshin Buhari sun hanashi haduwa da Buhari gaba da gaba.

“Suna tsorona ne saboda sun san na bankado satar naira Tiriliyan 1.3, kuma shugaban hukumar DSS ya bayyana cewa kamata yayi ayi amfani dani wajen gano wadannan kudade, don haka suke tsoron kada na hadu da Buhari har na fede masa biri har wustiya game da badakalar da suke tafkawa.

“Ina sane da wasu asusun bankin boye mallakin NNPC, kuma mutane 20 ne kacal suke da iko da wannan asusun, akwai wasu ire iren asusun bankunan nan kuma sun dade tsawon shekaru 15 zuwa 18, da wuya Buhari ya san dasu koda kuwa ya kai shekaru 10 a mulki.” Inji shi.

Daga karshe yayi karin haske game da zargin da Sanata Kabiru Gaya yayi masa, inda yace ya saci naira biliyan 195, yace bayan samun rahoton wannan zargi, ya kalubalanci Sanatan ya fayyace ma Najeriya gaskiyar yadda shi da takwarorinsa suka watanda da kudaden yan fansho idan ba haka ba zai fasa kwai.

“Kwatsam bayan wannan magana da nayi sai na ji shi a gidan talabijin yana wankeni, yana cewa ban saci ko sisi ba, kuma kudaden suna asusun bankin gwamnatin tarayya na bai daya, tun daga lokacin babu wanda ya kara zargina da satar kwabon yan Najeriya.” Inji shi.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Online view pixel