Oba Mufutau Olatunji Hamzat, basaraken gargajiya wato Olu na masarautar Afowora Sogade da ke jihar Ogun wanda ya kasance mahaifi ga zababben mataimakin gwamnan jihar Legas, Dakta Obafemi Hamzat, ya riga mu gidan gaskiya.

Marigayi Oba Mufutau Olatunji Hamzat
Source: UGC
Kamar yadda rahotanni suka bayyana a ranar Litinin, Oba Hamzat ya riga mu gidan gaskiya da Yammacin ranar Lahadin da ta gabata.
Marigayi Oba gabanin kasancewar sa Sarkin fadar Afowora Sogade da ke jihar Ogun shekaru kadan da suka gabata, ya kasance fitaccen dan siyasa a jihar Legas yayin da ya kasance daya daga cikin jiga-jigai na jam'iyyar AG (Action Group) da kuma UNP (United Party of Nigeria).
KARANTA KUMA: Ban ƙyale tayin gida ba don rijiyar burtsatsai a mahaifata - Mai gadi
Ya kasance jigo na jam'iyyar APC (All Progressive Congress) da kuma jam'iyyar AD (Alliance for Democracy) yayin dawowa tsarin mulkin dimokuradiyya a kasar Najeriya cikin shekarar 1999.
Zababben mataimakin gwamnan jihar Legas, Dakta Obafemi Hamzat yayin bayar da rahoton mai cike da bakin ciki, ya ce Mahaifin sa ya yiwa al'ummar jihar Legas gagarumar hidima da ba zata misaltu ba yayin kasancewar dan siyasa tun a shekarar 1979.
Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.android&pid=solomonovlink
Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com
Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta:
https://facebook.com/legitnghausa
https://twitter.com/legitnghausa
Ku fa'idantu da manhajar mu ta Azumi a wannan wata mai albarka a wannan shafi:
https://fb.gg/play/ramadan_ramadan