Ban ƙyale tayin gida ba don rijiyar burtsatsai a mahaifata - Mai gadi

Ban ƙyale tayin gida ba don rijiyar burtsatsai a mahaifata - Mai gadi

Kwanaki kadan da suka gabata ne kafofin sadarwa da dandalan sada zumunta suka kidime da labarin wani mai gadi Musa Usman da ya ƙyale tayi na karbar kyautar gida domin a ginawa al'ummar mahaifar sa rijiyar burtsatsai.

Sai dai yayin ganawar sa da manema labarai na jaridar Daily Trust a karshen makon da ya gabata, Musa Usman Mai gadi wanda ya fito daga rigar Fulani ta Giljimmi a yankin karamar hukumar Birniwa, yayin musanta rahoton ya fayyace gaskiyar yadda labarin sa ya kaya.

Rijiyar burtsatsai da Mista Pagis ya ginawa al'ummar mahaifar Musa Mai gadi
Rijiyar burtsatsai da Mista Pagis ya ginawa al'ummar mahaifar Musa Mai gadi
Source: UGC

Musa Mai gadi dai ya ce kyautatawa ta Ubangidan sa ya sanya bayan ya ziyarci mahaifar sa da ke jihar Jigawa ya yanke shawarar ginawa al'ummar sa rijiyar burtsatsai da ake matsananciyar bukatuwa zuwa gare ta.

A sakamakon rikon amana da tsayuwa kan gaskiya wajen yiwa Ubangidan sa Mista Pagis hidimar gadin gida ta tsawon shekaru 25 a jihar Legas, ya sanya Musa ya samu wannan sakayya ta sadaka mai gudana.

KARANTA KUMA: A shekarar 2023 zan janye jiki daga majalisar dattawa - Ekweremadu

Dangane da rahoton ya ƙyale tayin karbar kyautar gida a madadin a ginawa al'ummar mahaifar sa rijyar burtsatsai, Mallam Musa ya ce wannan kagaggen zance ne da ba ya da wata madogara ta gaskiya ballantana kuma tushe.

A yayin da a halin yanzu Musa yana ci gaba da yiwa Ubangidan sa hidima, ya ce babu batun ƙyale tayi na karbar kyautar gida a matsayin tukwicin rabuwar su da kuma sakayya ta bauta da yayi tsawon shekaru da dama da suka shude.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.android&pid=solomonovlink

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Ku fa'idantu da manhajar mu ta Azumi a wannan wata mai albarka a wannan shafi:

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit.ng

Online view pixel