Ku daina yi wa Mai shari’a Bulkachuwa sharri – Buhari ya fadawa PDP

Ku daina yi wa Mai shari’a Bulkachuwa sharri – Buhari ya fadawa PDP

Mun samu labari a Ranar 12 ga Watan Mayu cewa fadar shugaban kasa tayi kira ga jam’iyyar adawa ta PDP da ta daina dura kan shugaban kotun daukaka kara ta Najeriya, Mai shari’a Zainab Bulkachuwa.

PDP tana zargin Zainab Bulkachuwa, wanda ita ce shugaban Alkalan da ke sauraron karar zaben shugaban kasa na 2019, da yi wa jam’iyyar APC mai aiki. Mai magana da bakin shugaban kasa, Garba Shehu, yayi wannan jawabi.

Malam Garba Shehu yake cewa maganar da jam’iyyar PDP ta ke yi na cewa akwai wani bincike na hukumar DSS da ya taba nuna cewa an taba samun Alkali mai shari’a Zainab Bulkachuwa da aikata barna, sam ba gaskiya bane.

Shehu yake cewa wannan yana cikin sharrin da jam’iyyar adawa ta ke yi wa Alkalan kasar. Hadimin shugaban kasar yace PDP tana yin wannan ne da nufin kawo rikici tsakanin gwamnatin Shugaba Buhari da kuma masu shari’a.

KU KARANTA: Emefiele: Wata kungiya ta yabawa Shugaban kasa Buhari

Mai magana da yawun shugaban kasar yace babu wata ta-ta-bur-za da ake samu tsakanin shugaban kasa Muhammadu Buhari da Alkalan Najeriya a halin yanzu. Shehu yace don haka bai kamata a tasa Zainab Bulkachuwa da sharri ba.

A jawabin na shugaban kasar, Shehu yace bai dace PDP ta rika sukar Alkalai idan kotu tayi sakamakon da bai mata dadi ba, amma tayi tsit a duk lokacin da kotu tayi irin hukuncin da ta ke so. Malam Shehu yace hakan ya zama munafunci.

Jam’iyyar PDP tana kukan cewa bai kamata Zainab Bulkachuwa ta cigaba da jagorantar shari’ar shugaba Buhari da Atiku Abubakar a kotun zabe ba domin kusancin ta da jam’iyyar APC mai mulki.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit

Mailfire view pixel