A shekarar 2023 zan janye jiki daga majalisar dattawa - Ekweremadu

A shekarar 2023 zan janye jiki daga majalisar dattawa - Ekweremadu

Kamar yadda majiyar mu ta jaridar Daily Trust ta ruwaito, bayan sake samun nasara, mataimakin shugaban majalisar dattawan Najeriya, Ike Ekweremadu, ya yi karin haske na fayyace lokacin da zai yi ritaya daga kujerar sa ta Sanata.

A yayin da Sanata Ekweremadu ya samu nasarar lashe kujerar mai wakilcin shiyyar Enugu ta Yamma a zauren majalisar dattawan Najeriya karo na biyar, ya yanke shawarar cewa ba zai sake neman takarar kujerar ba daga wannan karo.

A shekarar 2023 zan janye jiki daga majalisar dattawa - Ekweremadu

A shekarar 2023 zan janye jiki daga majalisar dattawa - Ekweremadu
Source: Depositphotos

Sanata Ekweremadu mai wakilcin shiyyar Enugu ta Yamma a zauren majalisar dattawan kasar nan, ya yi wannan karin haske a ranar Lahadi, 12 ga watan Mayun 2019 yayin bikin murnar cikar sa shekaru 57 da aka gudanar a birnin Enugu.

Kamfanin dillancin labarai na Najeriya ya ruwaito cewa, Sanatan wanda ya kammala wa’adin sa na hudu a zauren majalisar dattawan kasar nan, ya sake samun nasarar lashe kujerar sa yayin babban zaben kasa da aka gudanar a ranar 23 ga watan Fabrairun 2019.

A yayin da wasu ke da akidar ba ka cin zamanin ka kuma ka ci na wani, dan majalisar cikin kalami nasa ya bayyana cewa, lokaci ya karato da ya kamata ya janye jiki daga majalisar tarayya domin baiwa wani sabon dan siyasar mai jini a jika dama yayin da zai kammala wa’adin sa na biyar a shekarar 2023.

KARANTA KUMA: Saraki zai gyara hanyoyi a mahaifar sa dake jihar Kwara

Ekweremadu ya ce shekaru 16 da ya shafe a zauren majalisar dattawan kasar nan ya ce hakar sa ta cimma ruwa wajen samun tasirin gaske ta fuskar riba da kuma romo da mazabar sa ta samu wajen aiwatar da ayyuka bila adadin.

Ya mika godiyar sa ga shugaban kasa Muhammadu Buhari a sanadiyar goyon baya a fuskar aikace-aikace da ya gudanar masu muhimmacin gaske wajen inganta ci gaba da bunkasar jin dadin rayuwar al’umma a mazabar sa.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.android&pid=solomonovlink

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Ku fa'idantu da manhajar mu ta Azumi a wannan wata mai albarka a wannan shafi:

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel