Saraki zai gyara hanyoyi a mahaifar sa dake jihar Kwara

Saraki zai gyara hanyoyi a mahaifar sa dake jihar Kwara

Shugaban majalisar dattawan Najeriya Abubakar Bukola Saraki, a ranar Lahadi, 12 ga watan Mayun 2019, ya kaddamar da katafaren aiki na inganta ci gaban gine-gine na hanyoyin yankin Omu-Aran a Mahaifar sa ta karamar hukumar Irepodun dake jihar Kwara.

Saraki wanda mataimakin shugaban ma’aikatan sa ya wakilta yayin kaddamar da babban aikin, Gbenga Makanjuola, ya ce hakan ya bayu ne domin inganta jin dadin al’umma mahaifar sa bisa tanadi na cika alkawarin da ya daukar masu.

Saraki zai gyara hanyoyi a mahaifar sa dake jihar Kwara

Saraki zai gyara hanyoyi a mahaifar sa dake jihar Kwara
Source: Depositphotos

Mista Gbenga ya yi kira na neman goyon bayan al’ummar yankin wajen bayar da hadin kai ga ma’aikata masu cin kwangilar aikin domin inganta ci gaban sa da kuma kammaluwa cikin gaggawa.

Tsohon gwamnan na jihar Kwara ya sha alwashin aiwatar da wasu muhimman ayyuka na ci gaba da inganta jin dadin al'ummar mahaifar sa. Ya misalta katafaren aikin na gyaran hanyoyi a matsayin somin tabi.

KARANTA KUMA: Dakaru sun halaka 'yan Boko Haram 4 a Maiduguri

Shugaban karamar hukumar Irepodun, Mista Muyiwa Oladipo, ya yabawa tagomashin shugaban majalisar dattawa kan al’ummar Mahaifar sa tare da cewar ya yi sara a kan gaba daidai da lokacin na mafificiyar bukata duba da yadda rashin ingatattun hanyoyi ya zamto ciwon akan a gare su.

A yayin da Saraki ya daura damarar tabbatuwar wannan aiki da manufa ta bunkasa harkokin kasuwanci na al’ummar sa, Sarkin gargagiya na yankin, Oba Abdulraheem Adeoti, ya bayyana farin cikin sa tare da yabawa Saraki a kan wannan sha tara ta arziki.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.android&pid=solomonovlink

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Ku fa'idantu da manhajar mu ta Azumi a wannan wata mai albarka a wannan shafi:

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit

Mailfire view pixel