Dawowar Sanusi II daga London: Kano ta dauki dumi, kanawa sun mamaye filin jirgi

Dawowar Sanusi II daga London: Kano ta dauki dumi, kanawa sun mamaye filin jirgi

Jama'ar jihar Kano sun yi tururuwa zuwa filin tashi da saukar jirage na Mallam Aminu Kano domin tarbar mai martaba sarki Sanusi II wanda zai dawo ake saka ran saukar sa daga kasar Ingila.

Daruruwan mutanen Kano sun yi dafifi da yammacin ranar Lahadi zuwa filin jirgin domin nuna soyayyar su da kauna ga sarki Sanusi II bayan gwamnatin jihar Kano ta raba masarautar Kano zuwa gida biyar.

Ana rade-radin cewar za a iya samun hargitsi saboda wasu masu goyon bayan gwamnati sun shirya gudanar da yin gangamin nuna wa sarki Sanusi goyon bayan su a kan matakin da gwamnatin jihar Kano ta dauka.

Kazalika, an zargi jami'an 'yan sanda da hana dandazon jama'ar tarbar sarki Sanusi kuma tsohon gwamnan babban bankin kasa (CBN).

Dawowar Sanusi II da London: Kano ta dauki dumi, kanawa sun mamaye filin jirgi

Sarki Sanusi II
Source: Twitter

Kwamishinan 'yan sandan jihar Kano, CP Mohammed Wakili, ya shiada wa majiyar mu cewar bai bayar da umarnin hana wasu jama'a gudanar da taron gangami ba, matukar sun yi hakan cikin lumana da zaman lafiya.

A ranar Laraba ne gwamna Ganduje ya rattaba hannu a kan dokar kirkirar sabbin masarautu hudu daga masarautar Kano.

DUBA WANNAN: Sabbin masarautu: Al'ummar karamar hukumar Wudil sun bijire wa Ganduje

A ranar Asabar ne gwamnan ya rantsar da sabbin sarakunan yanka na masarautu hudun da aka kirkira.

Sabbin masarautun su ne; Bichi, Gaya, Karaye da Rano.

Ana saka ran sarki Sanusi zai sauka a Kano da misalin karfe 4:15 na yamma, kamar yadda majiyar fada ta sanar.

Jama'a da dama, musamman masu adawa da matakin kirkirar sabbin masarautun da gwamnatin jihar Kano tayi, na jiran dawowar sarki Sanusi domin jin ta bakinsa ko matakin da zai dauka a kan abinda ya faru lokacin da baya nan.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.android&pid=solomonovlink

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel