Fayose: Shaidan Hukumar EFCC yayi amai ya lashe a gaban Kotu

Fayose: Shaidan Hukumar EFCC yayi amai ya lashe a gaban Kotu

Hukumar EFCC mai yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon-kasa, ta dakatar da karbar bayani daga bakin-shaidun da ta a wajen shari’ar ta da tsohon gwamnan jihar Ekiti, Ayodele Peter Fayose.

An gamu da abin mamaki a gaban kuliya a lokacin da hukumar EFCC ta kawo wanda ta ke so ya tsaya mata shaida wajen kama Ayo Fayose a gaban shari’a. Adewale Aladegbola shi ne wanda EFCC ta kawo yayi jawabi gaban Alkali.

Shaidan, wanda ma’aikacin banki ne ya nunawa kotu cewa bai san maganar da EFCC ta ke yi ba, inda ya bayyanawa Alkali cewa bai dauki wasu kudi daga banki a Ranar 16 Afrilun 2015 ba, kamar yadda EFCC ta ke kokarin rayawa ba.

Aladegbola wanda shi ne shaida na 13 da EFCC ta gabatar da kotu, ya kawowa binciken da EFCC ta ke yi cikas. EFCC tace an matsawa shaidan na ta lamba ne ya gaza fadawa Duniya gaskiyar abin da ya faru da tsohon gwamnan na Ekiti.

KU KARANTA: Babban abin da Buhari ya fi ba muhimmanci a kan mulki - Osinbajo

Fayose: Shaidan Hukumar EFCC yayi amai ya lashe a gaban Kotu

Hukumar EFCC na binciken tsohon Gwamna Fayose a Kotu
Source: Twitter

Babban Lauyan EFCC Rotimi Jacobs (SAN), ya so ace Aladegbola yayi wa kotu bayanin yadda ya dauki wasu makudan kudi a motarsa ta banki a babban birnin Ekiti na Garin Ado Ekiti wajen taimakawa tsohon gwamna Ayo Fayose.

Shaidan ya nunawa Kotu cewa sam bai yi aiki a Ranar da ake magana ba, don haka Lauyoyin EFCC su ka nemi shaidan ya dakata. Racob Jacobs yace shaidan na ta yayi magana biyu bayan a da ya bayyana badakalar wanda ake tuhuma.

Yanzu haka hukumar EFCC tana karar Ayo Fayose a gaban kotu da wasu laifuffuka 11. An fara shiga kotu da tsohon gwamnan ne a karshen 2018, wanda daga karshe aka bada belinsa a kan kudi Naira Miliyan 50.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit

Online view pixel