Manyan masu taimakawa Dankwambo sun daina samun albashi bayan zabe

Manyan masu taimakawa Dankwambo sun daina samun albashi bayan zabe

Jaridar Blue Print ta rahoto cewa gwamnan jihar Gombe, Ibrahim Hassan Dankwambo ya ki biyan Hadimansa da-dama albashi bayan da jam’iyyarsa ta PDP ta fadi zaben da aka yi bana a Najeriya.

Bayan jam’iyyar PDP ta sha kasa a hannun APC a zaben gwamna da na ‘yan majalisar tarayya a jihar Gombe, wadanda ke aiki da gwamna mai shirin barin-gado watau Ibrahim Dankwambo, ba su samu albashin watan da ya gabata ba.

Wani daga cikin wadannan masu ba gwamna shawara, yace duk wadanda gwamnan ya dauka aiki a matsayin Hadimansa kwanaki, ba su karbi albashin aikin su ba tun bayan da jam’iyyar PDP ta rasa mulki a hannun APC a Gombe.

Wannan Hadimi da ya ki bayyanawa ‘yan jarida sunansa, yace Hadimai 2000 da gwamnan ya dauka aiki a shekarar nan. Gwamna Dankwambo ya dauki mutane sama da 2000 aiki ne ana daf da zabe a matsayin masu ba sa shawara.

KU KARANTA: Shugaban kasa Buhari ya bar Ministocinsa a cikin duhu a 2019

Manyan masu taimakawa Dankwambo sun daina samun albashi bayan zabe

Ana so Gwamnan Gombe ya biya Ma’aikatansa kafin ya bar kan mulki
Source: UGC

Yanzu wadannan Hadimai na mai girma Dr. Ibrahim Hassan Dankwambo su na so Gwamnan na Gombe ya biya Ma’aikata 2000 da ya dauka aiki albashin wadannan watanni da aka yi kafin ya bar ofis a karshen wannan Wata na Mayu.

Wani daga cikin Mai ba gwamnan shawara yake cewa sau daya kurum aka biya sa albashinsa na N400, 000 tun da ya fara aiki, don haka yake kira ga gwamnan da ya taimaka ya biya su duk wani bashi da su ke bin gwamnati bayan zabe.

Makonni kusan 3 su ka rage a kafa sabon gwamnati a Najeriya, idan har wa’adin gwamnan ya shude ba tare da ya biya wadannan ma’aikata na sa albashi ba, zai yi wahala kudin aikin su ya fito. Da alama faduwa zaben yayi wa gwamnan zafi.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit.ng

Online view pixel