Babu abinda Buhari ya fi ba muhimmanci irin inganta jin dadin al'umma - Osinbajo

Babu abinda Buhari ya fi ba muhimmanci irin inganta jin dadin al'umma - Osinbajo

Mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo, ya jaddada tsayuwar daka ta shugaban kasa Muhammadu Buhari tare da bayar da mafificin fifiko mai muhimmancin gaske wajen inganta jin dadin rayuwar al'umma yayin riko da akalar da jagoranci.

Tsohon kwamishinan shari'a na jihar Legas ya bayyana cewa, nasarorin gwamnatin shugaban kasa Buhari musamman a bangaren shirye-shiryen bayar da tallafin zamantakewa manuniyace ta muhimmancin da ya bayar wajen inganta jin dadin al'umma.

Osinbajo tare da shugaban kasa Buhari da kuma jigon APC, Bola Tinubu

Osinbajo tare da shugaban kasa Buhari da kuma jigon APC, Bola Tinubu
Source: UGC

Osinbajo ya bayyana hakan ne a jihar Bauchi yayin kaddamar da wasu kananan masana'antu na man gyada da kuma sabulu baya ga aikin samar da wutar lantarki a yankunan karkara da gwamnatin jihar ta aiwatar.

A cewar Osinbajo, shugaban kasa Buhari zai ci gaba da dawwama kuma ba zai gushe ba wajen sanya fifikon muhimmanci a fagen inganta jin dadin rayuwar al'umma da a halin yanzu ya kasance babban jigo cikin akidu na gwamnatin sa.

Mataimakin shugaban kasar ya hikaito ire-iren shirin tallafi da gwamnatin shugaban kasa Buhari ta assassa da suka hadar da shirin N-Power, shirin ciyar da dalibai a makarantun Firamare, da kuma masana'antu da cibiyoyi kiwon lafiya da manufa ta dadadawa al'umma masu karamin karfi.

KARANTA KUMA: Buhari ba ya da haufi a kan wanda zai kasance shugaban majalisar dattawa - Aduwo

Majiyar jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, bayan isar sa Bauchin Yakubu, mataimakin shugaban kasa ya garzaya karamar hukumar Ningi inda ya kaddamar da katafaren aiki na samar da wutar lantarki musamman ga yankunan karkara na jihar.

Cikin jawaban sa na yabawa kwazon gwamnatin jihar Bauchi, Farfesa Osinbajo ya yi fashin baki da cewar kwazon gwamnatin jihar ya yi daidai da akidu na gwamnatin shugaban kasa Buhari wajen bunkasar ci gaban gine-gine.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.android&pid=solomonovlink

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Ku fa'idantu da manhajar mu ta Azumi a wannan wata mai albarka a wannan shafi: https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit.ng

Online view pixel