Mayar da Emefiele: Kungiyar AFAN ta jinjina wa Buhari

Mayar da Emefiele: Kungiyar AFAN ta jinjina wa Buhari

Kungiyar manoman Najeriya (AFAN) ta ce sake nada Godwin Emefiele a matsayin gwamnan babban bankin kasa CBN da Buhari ya yi, ya kara tabbatar da niyyar shugaban kasa na inganta harkar noma.

Cif Daniel Okafor, mataimakin shugaban kungiyar, ne ya fada wa manema labarai hakan a Abuja yayin da yake yabon Buhari a kan sake nada Emefiele.

Okafor ya roki Emefiele da ya cigaba da bawa manoma tallafi a karkashin shirin nan na ABP a zango na biyu da zai shugabanci CBN.

Kazalika ya bukaci gwamnan babban bankin da ya duba yiwuwar kara yiwa manoma ragi a kan ribar da suke dora wa a kan kudin da aka basu rance, ta koma tsakanin kaso uku zuwa biyar.

Mayar da Emefiele: Kungiyar AFAN ta jinjina wa Buhari
Godwin Emefiele
Asali: UGC

Okafor ya yi kira na musamman ga Emefiele da ya kara kirkirar wasu shirin bawa manoma ttallafi da kara yawan kudaden da ake bawa bankin manoma (BoA) domin manoma su kara samun rance kudaden da zasu inganta sana'o'in su.

DUBA WANNAN: Fitar da 100bn: Wani gwamna ya shiga tsaka mai wuya

"Mun ji dadin sake nada Emefiele a matsayin gwamnan CBN. Mu na mika godiya ga shugaban kasa a kan hakan.

"Hakan ya nuna cewa tabbas shugaban kasa da gaske yake yi a bangaren inganta harkar noma. Mu na yi masa godiya.

"Mu na son a cigaba da shirin ABP na bawa manoma rancen kudi a fadin kasar nan.

"Mu na kira ga majalisar tarayya da ta gaggauta tabbatar da Emefiele a matsayin gwamnan CBN a karo na biyu saboda manoma na bukatar sa a matsayin shugaban babban bankin kasa," a cewar Okafor.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.android&pid=solomonovlink

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel