2019: PDP za ta bar ‘Yan Majalisar Jam’iyyar APC a cikin duhu

2019: PDP za ta bar ‘Yan Majalisar Jam’iyyar APC a cikin duhu

Ana kishin-kishin cewa shugabannin jam’iyyar PDP, su yanke hukuncin cewa babu wani daga cikin ‘Yan majalisar ta da zai yi takarar shugaban majalisar dattawa ko kuma kakakin majalisar wakilai a bana.

Mu na samun labari daga Sunday Tribune cewa, PDP ta gagara cin ma matsaya a game da yadda za ta dumfari zaben ‘yan majalisan tarayya da za ayi a farkon Watan gobe. A farkon Yuni ne za a zabi shugabannin majalisa a kasar.

Daga cikin matakan da jam’iyyar hamayyar ta PDP ta dauka shi ne ba za ta sanar da Duniya, ‘yan takarar da za ta marawa baya ba tukuna. Za a kai ga lokacin zabe ne ba tare APC ta san wanda ‘Yan PDP za su zaba a wannan karo ba.

Sai ana daf da zaben ne shugabannin PDP za su zauna su fadawa ‘Ya ‘yan su wanda za su zaba a matsayin shugaban majalisar dattawa da shugaban majalisar wakilai na tarayya, kamar yadda rahoton na Tribune ya bayyana dazu.

KU KARANTA: 'Dan takarar Shugaba kasa a zaben 2019 ya caccaki Gwamna Ganduje

Majiyar ta bayyana cewa Jagororin PDP sun nemi ‘Yan majalisa na jam’iyyar adawar da su guji takarar kujera da duk wani ‘Dan majalisa na APC a zaben da za ayi. Hakan ya sabawa irin dabarun da jam’iyyar PDP tayi a lokacin zaben 2015.

Ana kishin-kishin din cewa Sanatocin PDP za su zabi Sanata Enyinnaya Abaribe a matsayin shugaban marasa rinjaye, yayin da Kakakin majalisa na yanzu watau Yakubu Dogara, zai rike takwarar wannan kujerar a majalisar wakilai a 2019.

Wannan tsari da PDP ta ke nema tayi a wannan karo, zai bata damar yi wa jam’iyyar APC mai mulki fito-na-fito a majalisar kasar ganin cewa babu ‘Ya ‘yan ta a cikin shugabannin majalisar da za su hana ta adawa.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit

Mailfire view pixel