An rasa yadda Shugaba Buhari zai zabo sababbin Ministoci

An rasa yadda Shugaba Buhari zai zabo sababbin Ministoci

A dogon taron FEC na Ministoci da aka yi a makon da ya gabata, shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya sake jefa dar-dar a zuciyar Ministocinsa a game da wadanda za su maye gurbin su a majalisar zartarwar.

Kamar yadda mu ka samu labari daga Jaridar Daily Trust ta Ranar 12 ga Watan Mayu, ana tunanin cewa wasu daga cikin Ministoci za su cigaba da rike mukamansu, ganin cewa shugaba Buhari bai da niyyar canza masu aiki da shi.

A cikin makon jiya ne ma dai shugaban kasa Buhari ya karawa gwamnan babban bankin kasar watau Godwin Emefiele wa’adin shekara 5 a ofis. Kan jama’a ya rabu sosai a game da wannan mataki da shugaba Buhari ya dauka.

Wasu na ganin cewa Godwin Emefiele yana da kafa a fadar shugaban kasar a dalilin kusancin da yake da shi da wasu na-hannun-daman Buhari. Wannan ya sa ake ganin cewa Ministocin kasar da ke da uwa a gindin murhu za su koma.

KU KARANTA: Gwamnati na na kokarin kawo karshen matsalar tsaro - Buhari

Rahoton ya nuna cewa ko da wasu Ministocin na Buhari ba su tabuka komai ba, za a iya kafa sabuwar gwamnati da su, muddin su na da wanda su ka tsaya masu a fadar shugaban kasa. A watan nan ne dai za a ruguza wannan gwamnati.

Akwai kuma masu tunanin cewa shugaban kasar zai kara yawan Ministocinsa, ana sa ran cewa Ministoci za su kara yawa daga 36 zuwa 42. Buhari ya nuna yiwuwar zakulo karin Minista guda daga kowane yankin kasar tun a 2017.

Wani da ke kusa da fadar shugaban kasar ya fadawa ‘yan jarida cewa duk abin da ake ji yana yawo a gari, jita-jita ne maras tushe. A cewar sa, babu wanda ya isa yace ga wadanda za su shuga cikin gwamnatin Buhari wannan karo.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit

Online view pixel