Buhari ba ya da haufi a kan wanda zai kasance shugaban majalisar dattawa - Aduwo

Buhari ba ya da haufi a kan wanda zai kasance shugaban majalisar dattawa - Aduwo

Jagoran wata kungiya mai fafutikar kare hakkin bil Adama, Kwamared Olufemi Aduwo, yayin ganawa da manema labarai ya yi karin haske kan matsayar shugaban kasa Muhammadu Buhari a kan jagorancin majalisar dattawa.

Kwamared Aduwo yayin amsa tambayoyin manema labarai ya ce, sabanin yadda ake ci gaba da ikirari kuma bisa madogara ta adalci, shugaban kasa Buhari ba ya da haufi dangane da wanda zai kasance jagora a sabuwar majalisar dattawan kasar nan.

Buhari ba ya da haufi a kan wanda zai kasance shugaban majalisar dattawa - Aduwo

Buhari ba ya da haufi a kan wanda zai kasance shugaban majalisar dattawa - Aduwo
Source: Twitter

Dangane da batun yaki da rashawa a Najeriya, Kwamared Aduwo ya ce ba bu abin da gwamnatin shugaban kasa Buhari ta sauya cikin kasar nan tun daga shekarar 2015 kawowa yanzu ta fuskar taka rawar gani a fagen yaki da rashawa.

Biyo bayan takkadamar jam'iyyar PDP yayin da jam'iyyar APC bisa jagorancin shugaban ta, Kwamared Adams Oshiomhole ta kebance kujerar jagoracin majalisar dattawa zuwa yankin Arewa maso Gabashin kasar nan, Kwamared Aduwo ya ce ko kadan shugaba Buhari ba ya da wata damuwa a kan wanda zai kasance sabon jagora a majalisar ta tarayya.

KARANTA KUMA: Ta'ddanci: Buhari zai biya kungiyar Miyetti Allah N100bn domin samar da wuraren kiwo

Da ya ke ci gaba da babatu a kan yaki da rashawa ta gwamnatin tarayya, kwamared Aduwo ya ce ba bu wata rawa da gwamnatin shugaban kasa Buhari ke takawa illa iyaka sanya idanun lura da binciken kwa-kwaf a kan dukiyar al'umma musamman attajirai.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.android&pid=solomonovlink

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Ku fa'idantu da manhajar mu ta Azumi a wannan wata mai albarka a wannan shafi: https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit

Online view pixel