Fitar da 100bn: Wani gwamna ya shiga tsaka mai wuya

Fitar da 100bn: Wani gwamna ya shiga tsaka mai wuya

Wani gwamna a Najeriya ya shiga tsaka mai wuya a kan fitar da zunzurutun kudi da yawan su ya kai kusan biliyan N100 daga asusun hadin gwuiwa na kananan hukumomin (SJLGA) da sunan yin amfani da su domin harkokin tsaro.

Jaridar The Nation ta rawaito cewar an fitar da madarar kudin ne daga asusun bisa umarnin gwamnan.

Wata hukuma mai bincike sirri a kan harkokin kudi (NFIU) ce ta bankado wannan badakala da ake zargin gwamnan da tafka wa.

Bankunan da aka yi amfani da su wajen fitar da wadannan kudade na taimakon hukumomi, musamman hukumar NFIU, a kan yadda aka tafka wannan badakala.

Wata majiya ta bayyana cewar binciken hukumar NFIU ya bankado badakalar da gwamnoni ke tafka wa da kudaden dake cikin asusun SJLGA.

Fitar da 100bn: Wani gwamna ya shiga tsaka mai wuya
Buhari da gwamnonin arewa
Source: Facebook

Wannan lamari ya jawo hukumar NFIU daukan matakin haramta wa bankuna, gwamnoni da cibiyoyin harkar kudi, da sauran masu ruwa da tsaki taba kudaden da ake turo wa kananan hukumomi daga asusn gwamnatin tarayya.

Wata majiya a NFIU ta ce: "mu na da shaidar yadda gwamnoni ke fitar da kudi daga asusun SJLGA, akwai gwamnan da ya fitar da kudin da yawan su ya kai biliyan N100. Lamarin ya faru ne a jihar dake fama da matsalolin tsaro.

DUBA WANNAN: An zo wurin: EFCC ta kwace wasu gidajen Saraki, ta saka wa wasu a Legas jan fenti

"Ya fitar da kimanin biliyan N10 a 'yan kwanakin baya bayan nan a cikin wani yanayi mai cike da alamomin tambaya.

"Mun sanar da dukkan hukumomin da ya dace wannan lamari, mun kuma ba su bayanai. Ba zamu bar irin wannan tabargaza ta cigaba da faruwa ba. Wasu daga cikin hukumomin tuni sun fara gudanar da bincike a kan wannan gwamna.

"Tun kafin hukumomin kasa da kasa su fara magana a kan irin wannan badakala, hukumar NFIU ta fara daukan matakan dakatar da bankuna daga bayar da hadin kai wajen aikada irin wannan almundahana."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.android&pid=solomonovlink

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Newspaper

Online view pixel