An zo wurin: EFCC ta kwace wasu gidajen Saraki, ta saka wa wasu a Legas jan fenti

An zo wurin: EFCC ta kwace wasu gidajen Saraki, ta saka wa wasu a Legas jan fenti

Jaridar Punch dake fitowa kowacce ranar Lahadi ta wallafa rahoton cewar hukumar yaki da cin hanci da karya tattalin arziki ta kwace wasu gidaje mallakar shugaban majalisar dattijai mai barin gado, Bukola Saraki.

Jaridar ta ce gidajen da aka kwace su ne masu lamba 15a, 15b da 17 dake kan titin Macdonald a unguwar Ikoyi a cikin kwaryar birnin garin Legas.

Sai dai, an gano cewar EFCC ba ta iya tantance wa da takamaiman gidajen dake zaman mallakar Saraki ba, lamarin da ya sa hukumar ta saka musu jan fenti tare da makala takardara a dukkanin idajen.

A yayin da Saraki ya ambaci gida mai lamba 15a da 15b a matsayin mallakin sa a cikin fom din bayyana kadarori, hukumar EFCC na zargin cewar ya sayi arin wasu makwabatn gidaje ta hannun kamfanin man fetur na Shell a karkashin shirin fadar shugaban kasa na sayar da kadarorin gwamnati.

An zo wurin: EFCC ta kwace wasu gidajen Saraki, ta saka wa wasu a Legas jan fenti
EFCC ta kwace wasu gidajen Saraki, ta saka wa wasu ja fenti a Legas
Source: Twitter

Wani dan uwan Saraki, da ya bukaci a boye sunan sa, ya ce hukumar EFCC ta garkame gidajen ne ranar juma'a.

Ya bayyana cewar hukumar EFCC ta dade da fara bincike a kan kadarori da kudaden da Saraki ya mallaka.

"EFCC ta wana biyu da fara bincike a kan kadarori da kudaden da Saraki ya mallaka. Sun zo sun yi rubutu da jen fenti a bangon wasu gidaje da suka hada da wadanda ba mallakinsa ba.

DUBA WANNAN: Sabbin Sarakuna: Mun yiwa dokar garambawul, babu mai iya canja ta - Ganduje

"Mun samu labari daga majiya mai tushe cewar hukumar EFCC ta saka ido a kan Saraki domin gayyatar sa ofishinsu da zarar an kammala tantsar da sabbin zababbun masu mulki a ranar 29 ga watan Mayu," a cewar dan uwan Saraki.

A lokacin da EFCC ta gurfanar da shi a shekarar 2016 a gaban kotun da'ar ma'aikata, EFCC ta shaida wa kotun cewar Saraki ya mallaki wasu gidaje a kan titin Macdonald, amma tayi zargin cewar bai bayar da cikakken adireshin su ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.android&pid=solomonovlink

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel