Sabbin Sarakuna: Mun yiwa dokar garambawul, babu mai iya canja ta - Ganduje

Sabbin Sarakuna: Mun yiwa dokar garambawul, babu mai iya canja ta - Ganduje

Gwamnan jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya garambawul din da aka yiwa dokar nadi da sauke sarakuna a shekarar 2019 ba zai warwaru ba, saboda yadda aka yiwa dokar tankade da rairaya.

Ganduje ya fadi hakan ne yayin bikin nuna jin dadi da yi masa godiya da sabbin sarakunan Rano, Bichi da Karaye suka shirya.

Gwamna Ganduje ya buaci dukkan hakimai da manyan limamai dake karkashin sabbin masarautun, da su yi musu mubaya'a ranar Lahadi.

Ya yi kira ga sabbin sarakunan da su mayar da hankali wajen bawa jama'a jama'a karfin rungumar noman rani da na damina, kiwon lafiya, da neman ilimi.

"Ku tabbatar jama'ar ku sun tura yaran su makaranta, mata kuma sun ziyarci asibiti a lokacin da suka samu juna biyu.

Sabbin Sarakuna: Mun yiwa dokar garambawul, babu mai iya canja ta - Ganduje

Ganduje da mataimakinsa a wurin bikin nada sabbin sarakuna a jihar Kano
Source: Facebook

"Mun gano shirin wasu batagari na gudanar da zanga-zanga. Zasu yi hakan ne domin haddasa rashin zaman lafiya a Kano, amma hakan ko kadan ba zai saka mu canja ra'ayinmu a kan kirkirar sabbin masarautun ba.

"Mun kirkiri sabbin sarakunan yanka ne domin rage wa masarautar Kano nauyin dake kan ta. Nauyin ya yiwa masarautar yawa, hakan ne ma ya sa muka kirkiri wasu domin a rage mata nauyi," a cewar Ganduje.

DUBA WANNAN: Abinda Buhari ya fada wa shugabannin hukumomin tsaro yayin ganawar su

Sannan ya cigaba da cewa; "kirkirar sabbin masarautun tamkar sake waiwayar tarihi ne. Wannan ba wani sabon abu ba ne a Kano, hakan ta taba kasancewa a baya.

"Mun kirkiri sbbin masarautun ne domin amsa bukatar mutanen mu. Na tabbata yin hakan zai kawo cigaba cikin sauri ga yankunan karkara."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.android&pid=solomonovlink

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel