Boko Haram: An kashe mutum 4, an sace 5 a Maiduguri

Boko Haram: An kashe mutum 4, an sace 5 a Maiduguri

- Mayakan Boko Haram sun sake kai hari a Maiduguri sun jefa al'ummar garin cikin dimuwa

- 'Yan ta'addan sun kai farmaki a Njimtilo a garin Maiduguri inda suka kashe mutane kuma suna sace kayan abinci

- Rahotannin sun ce 'yan ta'addan sun kashe mutum biyar kuma an sun sace ma'aikatan Airtel guda biyar

A ranar Asabar 11 ga watan Fabrairu ne mayakan kungiyar Boko Haram suka kai hari a Maiduguri babban birnin jihar Borno, inda suka kashe mutane biyar kuma suka jikatta wasu da dama.

Wani mazaunin garin, Prophet Sunday Solomon ya ce 'yan ta'addan sun kawo farmaki gidansa da ke Njimtilo a Maiduguri inda suke kashe mutane kuma suka yi awon gaba da kayayakin abinci da wasu abubuwa masu muhimmanci kamar yadda This Day ta ruwaito.

Boko Haram: An kashe mutum 4, an sace 5 a Maiduguri

Boko Haram: An kashe mutum 4, an sace 5 a Maiduguri
Source: UGC

DUBA WANNAN: Gwamnonin APC sun karrama Buhari da lambar yabo (Hoto)

Solomon wanda ya sha da kyar bayan wata harsashi ta shafi shi ya ce Allah ne ya kiyaye shi kuma shi da iyalansa suka buya yayin da suka ji harbe-harben bindiga da 'yan ta'addan ke yi.

Ya kara da cewa 'yan ta'addan sunyi tafiyarsu bayan aikata mummunan barna tare da sace wayoyin salula da kayan abinci.

Wani shaidan ganin ido Pete Ogeleh wanda aka kai masa hari a gidansa ya ce 'yan ta'addan sunyi awon gaba da wani Isaac Dibal da wasu mutanen hudu ma'aikatan kamfanin sadarwa na Airtel.

Bello Danbatta, Shugaban hukumar bayar da agajin gaggawa na jihar Borno, ya ce gawar mutane hudun da suka rasu suna dakin ajiye gawa na asibitin sannan sauran mutanen da sika jikkata suna samun kulawa a asibitin kwararru na jihar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku Latsa: Domin karuwa cikin wannan wata mai albarka na Ramadana

Source: Legit

Mailfire view pixel