Da dumi duminsa: Dan shekara 15 ya kafa tarihi a jarabawar JAMB ta 2019 da maki 347

Da dumi duminsa: Dan shekara 15 ya kafa tarihi a jarabawar JAMB ta 2019 da maki 347

-Wani Yaro dan shekara 15 ya kafa tarihi a jarabawar JAMB ta 2019 inda ya samu maki 347

-Wanda ke bi masa a mataki na biyu ya samu maki 346 yayinda na ukunsu ya samu maki 345

Ekene Franklin dan asalin jihar Abia mai shekaru 15 da haihuwa ya kafa tarihi a jarabawar JAMB ta 2019 inda ya samu maki 347 a sakamakon jarabawar da aka fitar ranar Assabar.

Da dumi duminsa: Dan shekara 15 ya kafa tarihi a jarabawar JAMB ta 2019 da maki 347

Da dumi duminsa: Dan shekara 15 ya kafa tarihi a jarabawar JAMB ta 2019 da maki 347
Source: Depositphotos

KU KARANTA:Zamu yi aiki tareda yan sintiri da mafarauta saboda karancin jami’an yan sanda - Kwamishanan yan sanda

Wanda yazo mataki na biyu wani yarone mai shekaru 16 da haihuwa wanda ya fito daga jihar ta Abia inda ya samu maki 346, sai wanda yazo mataki na uku da maki 345 dan jihar Osun mai suna Olamilekan Oloyode.

Sai dai shugaban hukumar JAMB Farfesa Ishak Oloyode wanda ya shaidawa manema labarai yayin wata tattaunawa ta musamman yace yaron da yazo na daya a jarabawar ba zai samu gurbin karatu ba a jami’ar Legas wacce itace yake son zuwa saboda shekarunsa.

A wani labari mai kama da wannan, gwamna Abdullahi Umar Ganduje na jihar Kano yace babu 'yar tsama tsakaninsa da Sarki Sanusi.

Zancen ya biyo bayan zargin da jama'a ke tayi na cewa da gayya gwamnan ya rarraba masarautar ta Kano zuwa kashi biyar. A cewar gwamnan ," Sarki kamata yayi ace yana karkashin shugaban karamar hukuma ba gwamna ba a bisa kundin tsarin mulkin Najeriya."

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

KU LATSA : Domin karuwa cikin wannan wata mai albarka na Ramadan

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel