Yan daba sun tarwatsa masu zanga-zangan nuna rashin goyon bayan raba masarautar Kano

Yan daba sun tarwatsa masu zanga-zangan nuna rashin goyon bayan raba masarautar Kano

Wasu matasa da suka da maza da mata sun shirya gudanar da wata zanga-zanga don nuna rashin goyon bayan kacaccala masarautun Kano a yau Asabar, 11 ga watan Mayu.

Sun shirya wannan gangami ne a karkashin inuwar kugiyar “Kano First.”

Masu zanga-zangar sun shirya taruwa ne a harabar Kofar Kwaru da ke gidan sarkin Kano, daga nan sai su yi tattaki zuwa harabar gidan gwamnatin jihar don nuna adawarsu ga yunkurin gwamnatin jihar karkashin Abdullahi Ganduje.

Sai dai hakan bai yi wu ba sakamakon wasu da ake zargin 'yan daba ne suka mamaye gurin tun da sanyin safiya dauke da manyan hotunan Sabon Sarkin Bichi Aminu Ado Bayero da na Marigayi Sarki Ado Bayero.

Yan daba sun tarwatsa masu zanga-zangan nuna rashin goyon bayan raba masarautar Kano

Yan daba sun tarwatsa masu zanga-zangan nuna rashin goyon bayan raba masarautar Kano
Source: UGC

Sakamakon haka ne ya tursasa wa masu zanga-zangar koma wa bakin kotun Kofar Kudu da ke kallon gidan sarkin Kano domin gudanar da taron na su wanda shi ma daga baya aka tarwatsa su.

KU KARANTA KUMA: Ba gudu ba ja da baya: Ganduje zai nada sabbin sarakuna - Gwamnatin Kano

Yan daba sun tarwatsa masu zanga-zangan nuna rashin goyon bayan raba masarautar Kano

Yan daba sun tarwatsa masu zanga-zangan nuna rashin goyon bayan raba masarautar Kano
Source: UGC

Gwamnatin jihar ta tsayar da ranar Asabar a matsayin ranar da za a mika takardar kama aiki ga sabbin sarakunan da aka kirkiro a jihar ta Kano, duk da cewar wata babbbar kotun jihar a ranar Juma'a ta bayar da umarnin a dakatar da rantsarwar tare kuma da kirkiro wasu masarautu, amma wasu rahotanin sun nuna cewar gwamnatin jihar ta ce bata sami takardar umarnin Kotun ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Ku latsa domin karuwa cikin wannan wata mai albarka na Ramadana: https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel