Mahaifin wasu yara 3 da aka sace ya ki amincewa ya biya fansa

Mahaifin wasu yara 3 da aka sace ya ki amincewa ya biya fansa

-Mahaifin wasu yara 3 yacewa masu garkuwar da suka dauke yaransa cewa shi ba zai biya kudin fansa akan yaran ba

-Kimanin mako 3 da suka wuce ne akayi awon gaba da yaran akan hanyar Wukari zuwa Takum

Wani hamshakin dan kasuwa dake zaune a garin Ibbi dake jihar Taraba mai suna Alhaji Bakon Dare yaki amincewa ya biya N30m a matsayin fansar diyansu 3 da aka sace.

An sace yaran nasa akan hanyar dake tsakanin Wukari zuwa Takum a mako uku da suka shude. Wadanda sukayi garkuwa da yaran sun kirashi akan ya kawo fansar N30m amma yaki sauraronsu.

Mahaifin wasu yara 3 da aka sace ya ki amincewa ya biya fansa

Mahaifin wasu yara 3 da aka sace ya ki amincewa ya biya fansa
Source: UGC

KU KARANTA:Zamu yi aiki tareda yan sintiri da mafarauta saboda karancin jami’an yan sanda - Kwamishanan yan sanda

Wani dan uwan wannan mutum, Musa Ibbi shine ya baiwa jaridar Daily Trust labarin cewa, mutumin ya fadawa masu garkuwar cewa shi ba zai biya wani kudin fansa domin a saki yaransa.

A wani labari mai kama da wannan kuwa, wani dan bindigane ya kai hari masallacin Landan yayinda ake sallar taraweeh.

Wannan mutum wanda yaje masallacin Seven Kings dake Landan da fuskarsa a rufe dauke da bindiga, yayi harbi amma bai samu kowa ba. A karshe masu gadin masallacin ne sukayi nasarar korarsa daga masallacin.

Wani dan bindiga ya kai hari masallacin Landan yayinda ake sallar taraweeh

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

KU LATSA : Domin karuwa cikin wannan wata mai albarka na Ramadan

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel