Karin albashi: An gargadi 'yan kasuwa game da karin farashin kayayaki

Karin albashi: An gargadi 'yan kasuwa game da karin farashin kayayaki

- Shugaban kungiyar 'yan kasuwa na kasa (NANTS) ya gargadi 'ya'yan kungiyan game da yin karin farashin kayayaki saboda karin albashi

- Shugaban NANTS, Ken Ukaoha ya yi wannan kiran ne a wurin taron bayar da horo da shugabanin kungiyoyin 'yan kasuwa da aka gudanar a Katsina

- Ukaoha ya ce kara farashin kayayaki ba tare da dalili ba zalunci ne kuma ba abinda zai haifar ila talauci da fatara

Karin albashi: An gargadi 'yan kasuwa game da karin farashin kayayyaki

Karin albashi: An gargadi 'yan kasuwa game da karin farashin kayayyaki
Source: UGC

Kungiyar 'yan kasuwa na kasa (NANTS) ta gargadi mambobinta su kauracewa yin karin farashin kayayaki saboda ganin an samu karin albashi mafi karanci ga ma'aikatan Najeriya.

A jawabin da ya yi wurin taron karawa juna ilimi da aka shiryawa shugabanin NANTS domin bibiyar nasarorin da ake samu a kan tallafin da 'yan siyasa ke bawa manoma da 'yan kasuwa a Katsina, shugaban kungiyar na kasa, Ken Ukaoha ya ce yin karfin farashi ba tare da wani dalili ba zalunci ne da rashin sanin ya kamata.

DUBA WANNAN: An cafke wani ya yi sata a kamfanin Dangote

Ya ce da zarar 'yan kasuwa sun kara farashin kayayakin su, abinda hakan zai haifar shine karuwar bakin talauci da fatara a kasar.

A baya, Legit.ng ta ruwaito muku cewa shugaba Muhammadu Buhari ya rabbata hannu kan dokar karin albashi mafi karanci na naira 30,000 a Najeriya.

Hakan yana nufin daga yanzu N30,000 shi ne albashi mafi karanci da ma’aikata za su karba a fadin Najeriya, kamar yadda fadar shugaban ta bayyana a shafinta na Twitter ranar Alhamis.

“Shugaba Buhari ya sanya wa sabuwar dokar mafi karancin albashi hannu. Daga yanzu N30,000 ne mafi karancin albashin,” inji sanarwar.

Sanarwar ta kara da cewa “dokar za ta fara aiki nan take kuma ta shafi kowane ma’aikaci.”

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku latsa: Domin karuwa cikin wannan wata mai albarka na Ramadana

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel