Ba gudu ba ja da baya: Ganduje zai nada sabbin sarakuna - Gwamnatin Kano

Ba gudu ba ja da baya: Ganduje zai nada sabbin sarakuna - Gwamnatin Kano

Gwamnatin jihar Kano ta ce babu ja da baya a kan batun naddin sabbin sarakuna hudu duk da umurnin kotu da aka bayar da dakatar da nadin sarautan.

Cikin wata sanarwa da babban sakataren yada labarai na gwamnan Kano, Abba Anwar ya fitar a ranar Asabar, ya ce an riga an mikawa sabbin sarakunan wasikun kama aiki tun kafin kotun ta dakatar da nadin.

Sanarwar ta kara da cewa gwamnatin jihar Kano ba ta samu wani umurni daga kotu ba na hana ta cigaba da naddin sabbin sarakunan masu daraja ta daya na masarautun Rano, Karaye, Gaya da Bichi.

Ba gudu ba ja da baya: Ganduje zai nada sabbin sarakuna - Gwamnatin Kano

Ba gudu ba ja da baya: Ganduje zai nada sabbin sarakuna - Gwamnatin Kano
Source: Facebook

DUBA WANNAN: An cafke wani ya yi sata a kamfanin Dangote

Anwar ya ce: "Umurnin na kotu ya fara aiki ne bayan karfe 5 na yammacin ranar Juma'a 10 ga watan Mayun 2019 amma dukkan sabbin sarakunan sun amince da wasikun nadin sarautun tsakanin karfe 10 zuwa 12 ranar Juma'a kafin kotun ta bayar da umurnin dakatarwar.

"Sabon sarkin Karaye, Alhaji Dr Ibrahim Abubakar II ya ratabba hannu kan wasikarsa misalin karfe 12 na rana, Sarkin Rano Tafida Abubakar Ila ya saka hannu a wasikarsa karfe 10:15 na safe, Sarkin Bichi, Alhaji Aminu Ado Bayero ya rattaba hannu kan wasikarsa misalin karfe 10 yayin da Sarkin Gaya, Alhaji Ibrahim Abdulkadir ya rattaba hannu kan wasikarsa misalin karfe 10:30 na safe.

"Taron da za a gudanar a yau Asabar 11 ga watan Mayun 2019 a filin motsa jiki na Sani Abacha da ke Kofar Mata kawai an shirya ne domin sabbin bayar da wasikun nadin a bainar Jama'a tare da bawa sarakunan damar yiwa gwamna godiya bisa damar da ya basu na yiwa Jama'arsu hidima."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku Latsa: Domin karuwa cikin wannan wata mai albarka na Ramadana

Source: Legit Nigeria

Online view pixel