Wani dan bindiga ya kai hari masallacin Landan yayinda ake sallar taraweeh

Wani dan bindiga ya kai hari masallacin Landan yayinda ake sallar taraweeh

-Dan bindiga rufe da fuska ya kai hari masallacin Seven Kings dake birnin Landan

-Wadanda ke masallacin a lokacin aukuwar wannan al'amari sun tabbatar mana cewa babu wanda ya samu rauni ko kuma ya mutu sakamakon harin

Rahotanni sun nuna cewa al’ummar musulmi sun hadu a masallacin Seven Kings dake Landan domin yin sallar taraweeh yayinda suka fara jin sautin bindiga daga wajen masallacin.

Daga nan ne, dan bindigan ya samu damar shiga masallacin ta hanyar babbar kofar shiga masallacin amma sai dai anyi nasarar korarsa kafin ya sake yin wani harbin.

Wani dan bindiga ya kai hari masallacin Landan yayi da ake sallar taraweeh

Wani dan bindiga ya kai hari masallacin Landan yayi da ake sallar taraweeh
Source: Twitter

KU KARANTA:Ba abinda ke tsakanina da Sarki Sanusi, inji Ganduje

Wata hukuma wacce ta gudanar da bincike akan lamarin tace, tabbas anyi harbin bindiga amma dai babu wanda ya samu ko rauni a sakamakon harbin. Bincike ya sake tabbatar mana da cewa babu ta inda masallacin ya samu nakasu a sanadiyar harbin.

Ibrahim Hussain dan shekara 19 wanda yake masallacin lokacin aukuwar lamarin yace, “ Masallacin yanada sashe guda 3, cikin watan Ramadana musamman lokacin sallar taraweeh masallacin na cika makil.

“ Muna gidan sama cikin wani aji kimanin minti 30 da fara sallarmu kawai sai muka ji wata kara mai firgitarwa. Bamu damu ba muka cigaba da sallar da mukeyi, karar da muka ji dai tayi kama da karar fashewar wani abu. Bayan mun idar da sallar zamu sanya takalma ne wani ke fada mana ai karar harbin bindiga ce.

“ Masu kula da masallacin sun ganshi rufe da fuska ga kuma bindiga a hannu, tabbas ya harba bindigar tasa amma bai samu kowa ba. A karshe sai gudu yayi ya bar masallacin sanadiyar korarsa da masu gadi sukayi.” A cewar Ibrahim.

Limamin wannan masallaci, Mufti Suhail ya tabbatar mana da aukuwar wannan al’amari inda yace: “ An samu harin bindiga a masallacin Seven Kings a lokacin sallar taraweeh. Sai dai wanda ya kawo harin bai samu nasara ba saboda masu gadin masallacin sunyi galaba a kansa inda suka kora shi ya tafi. Ya dai yi harbi amma bai samu ko mutum guda ba.” Inji limamin masallacin.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

KU LATSA : Domin karuwa cikin wannan wata mai albarka na Ramadan

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel