Sababbin masarautun Kano: Abinda yasa kotu ta dakatar da Ganduje

Sababbin masarautun Kano: Abinda yasa kotu ta dakatar da Ganduje

- Jiya Juma'a ne dai wata kotu a jihar Kano ta dakatar da yunkurin da gwamnan Kano Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya ke yi na kirkiro da sababbin masarautu guda hudu a fadin jihar

- Kotun ta bayar da wannan umarnin ne bayan kara da Rabiu Sule Gwarzo ya shigar inda yake kalubalantar gwamnan jihar akan yunkurin da yake yi

A jiya Juma'a ne wata Kotun Koli a jihar Kano da ke unguwar Ungogo ta dakatar da gwamnan jihar Dr. Abdullahi Umar Ganduje daga daukar matakin raba masarautar jihar zuwa gida biyar.

Masarautun da gwamnan zai kara guda hudu sun hada da Masarautar Rano, Masarautar Bichi, Masarautar Gaya da kuma Masarautar Karaye.

Umarnin kotun ya biyo bayan karar da Rabi'u Sule Gwarzo ya kai inda yake kalubalantar gwamnan jihar akan yunkurin shi na kirkiro sababbin masarautu hudu a jihar.

Sababbin masarautun Kano: Abinda yasa kotu ta dakatar da Ganduje

Sababbin masarautun Kano: Abinda yasa kotu ta dakatar da Ganduje
Source: Facebook

Alkalin kotun, mai shari'a Nasiru Saminu, ya ba da umarni ga dukkanin masu hannu a lamarin akan su saurara domin a tabbatar da yiwuwar hakan.

Bayan haka kuma, mai shari'a Saminu, ya ba da umarni ga gwamnan jihar da kuma masu buga takardu na gwamnati akan su dakata da wallafa dukkanin takardu da suke da alaka da sababbin masarautun.

Mai gabatar da karar shi ne Rabiu Sule Gwarzo, yayin da kakakin majalisar jihar ya ke kalubalantar karar.

KU KARANTA: 'Yar gidan Sarkin Kano ta mayarwa da Ganduje raddi

Bugu da kari, majalisar dokokin Kano ita ce mai kalubalantar kara ta biyu, sai gwamnan jihar Abdullahi Umar Ganduje a matsayin na uku da zai kalubalanci karar, alkalin alkalan jihar kuma kwamishinan shari'a na jihar shine na hudu da zai kalubalanci karar sai kuma masu wallafa takardu na gidan gwamnatin Kano a matsayin na biyar.

Alkalin kotun ya bayyana ranar Laraba 15 ga watan Mayu a matsayin ranar da za a cigaba da sauraron karar da kuma albarkacin bakin jama'a.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa nan: Domin karuwa cikin wannan wata mai alfarma na Ramadana

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel