Dan takarar shugaban kasa ya saka baki cikin kirkirar sabbin masarautun Kano

Dan takarar shugaban kasa ya saka baki cikin kirkirar sabbin masarautun Kano

- Kingsley Moghalu ya yi tsokaci a kan kirkiran sabbin masarautu hudu da gwamna Abdullahi Ganduje ya yi

- Dan takarar shugaban kasar na YPP a zaben 2019, ya ce an kirkiri masarautun ne domin rage karfin mulkin Sanusi da kuma hana shi fadin gaskiya

- Dan takarar shugaban kasar kuma ya bukaci a sauya tsarin rabon arzikin kasa ta yadda za a bawa sarakunan gargajiya ikon bayar da shawarwari domin cigaban kasa

Kingsley Moghalu ya soki kirkiran sabbin masarautu hudu a Kano da Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya yi inda ya kira shi yunkuri ne na rage karfin kujerar Sanusi saboda dalilan siyasa.

Moghalu, wanda dan takarar shugaban kasa ne na jam'iyyar Young Progressives Party (YPP) a zaben 2019, ya yi wannan furucin ne a ranar Juma'a 10 ga watan Mayu yayin da ya ke jawabi a wurin taron Sikiru Kayode Adetona kamar yadda The Cable ta ruwaito.

Tsohon mataimakin gwamna na CBN ya ce abinda ya faru a Kano yunkuri ne na dakile masu fadin gaskiya.

Ganduje ya kacacala masarautar Kano ne domin muzanta Sanusi - Moghalu
Ganduje ya kacacala masarautar Kano ne domin muzanta Sanusi - Moghalu
Source: Twitter

DUBA WANNAN: An cafke wani ya yi sata a kamfanin Dangote

Ya kuma ce jama'a ne ya dace su zabi sarakunan gargajiya ba gwamnonin jihohi ba.

Ya ce: "Mun ga wani abu da ya faru a Kano a 'yan kwanakin nan, An kacacala masarautar Sarki kuma an ci mutuncin sarauta.

"Mun san dalilin da yasa aka aikata hakan; domin a dakile muryar da ke fadin gaskiya.

"Bai dace gwamnatoci su rika nada masu sarautun gargajiya ba. Jama'a ya da ce su zabi sarakunan su sannan gwamnati ta amince da su."

Moghalu ya nuna rashin jin dadinsa kan yadda aka mayar da masu sarautun gargajiya 'yan aiken gwamnati hakan yasa ya yi kira da a yiwa kundin tsarin mulkin Najeriya garambawul ta yadda za a bawa sarakuna aiki na bayar da shawarwari.

Ya ce: "Idan an yiwa kudin tsarin mulkin Najeriya garambawul, ya da ce a bawa masu sarautun gargajiya aikinsu na matsayin masu bayar da shawarwari. Wannan shine abinda ya da ce muyi. Bai da ce a mayar da sarakuna 'yan sakon 'yan siyasa ba ta yadda idan ba su yi abinda suke so ba za su rika yi musu bita da kulli."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku latsa: Domin karuwa cikin wannan wata mai albarka na Ramadana

Source: Legit

Online view pixel