Rundunar yan sanda ta kama masu garkuwa da mutane guda 157

Rundunar yan sanda ta kama masu garkuwa da mutane guda 157

Sufeto janar na rundunan yan sandan Najeriya (IGP) Mohammed Adamu a jiya Juma’a, 10 ga watan Mayu ya bayyana cewa masu garkuwa da mutane 157 ne aka kama a fadin kasar a watan Afrilu, yayin da aka kama 13 a makon farko a watan Mayu.

Ya ce bayanai akan laifuffukan kasar daga ranar 1 ga watan Afrilu ya nuna cewa yan sandan na cigaba da samun nasara wajen kame-kamen masu laifi tare da kwato bindigogi tun daga lokacin da aka soma aikin Operation Puff Adder.

Adamu ya fadi hakan ne a tattaunawa da yayi tare da manyan jami’an yan sanda a dakin ganawa na IGP, a hedikwatan hukumar, da ke Abuja.

Rundunar yan sanda ta kama masu garkuwa da mutane guda 157

Rundunar yan sanda ta kama masu garkuwa da mutane guda 157
Source: Depositphotos

Yace jihar Kaduna ta kasance akan gaba a kame-kamen masu garkuwa da aka yi tare da masu laifi 18, sai jihar Filato mai mai masu laifi 17, Edo 15 sannan Niger da Zamfara kowannensu ta kasance da 10.

KU KARANTA KUMA: Ban karbi wani umurni daga kotu kan nada sabbin sarakuna ba - Kwamishinan shari'ah na Kano

Shugaban yan sandan har ila yau dai yace an kama yan fashi da makami 218 a ayyuka da dama wanda rundunan yan sanda ta gudanar a reshe daban daban a watan Afrilu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku latsa domin karuwa cikin wannan wata mai albarka na Ramadana: https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel