Da duminsa: JAMB ta saki sakamakon jarrabawar 2019

Da duminsa: JAMB ta saki sakamakon jarrabawar 2019

- Yanzu nan muke samun labarin cewa hukumar JAMB ta fitar da sakamakon jarrabawar dalibai na wannan shekarar

- Sai dai hukumar ta bayar da sanarwar ba duka sakamakon ta fitar ba, ta rike wasu kimanin 34,120, wanda ta ke zargi da aikata satar amsa

- An samu jinkirin kin sakin sakamakon jarrabawar ne bayan hukumar ta fuskanci cewa da yawan daliban da suka rubuta jarrabawar sun saci amsa

Hukumar JAMB ta saki sakamakon jarrabawar dalibai masu neman cigaba da karatu a jami'a.

Hukumar ta saki kimanin sakamakon mutane miliyan 1,792,719 wadanda suka zana jarrabawar, yayin da ta rike sakamakon jarrabawar mutane 34,120 wadanda ake zargi da aikata satar jarrabawa.

Da duminsa: JAMB ta saki sakamakon jarrabawar 2019

Da duminsa: JAMB ta saki sakamakon jarrabawar 2019
Source: Depositphotos

Rijistara na hukumar, Farfesa Ishaq Oloyede, shi ne ya sanar da hakan yau Asabar dinnan a Abuja, ya kuma bayyana cewa sakamakon mutane 15,145 an rike shi ne domin kara tabbatar da gaskiyar su.

KU KARANTA: 'Yar gidan Sarkin Kano ta mayarwa da Ganduje raddi

A jiya Juma'a ne dai hukumar taa bayyana cewa yau za ta saki sakamakon daliban.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa nan: Domin karuwa cikin wannan wata mai alfarma na Ramadana

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel