Mafi karancin albashi: Kungiyar kwadago tayi gargadi ga gwamnatin tarayya

Mafi karancin albashi: Kungiyar kwadago tayi gargadi ga gwamnatin tarayya

-Kungiyar kwadago ta gargadi gwamnati akan rashin biyan sabon mafi karancin albashi

-Bayan da shugaba Buhari ya riga ya sanya hannu kan dokar biyan N30,000 matsayin mafi karancin albashi har yaznu ma'aikata na jiran yaushe za'a fara biyansu

Akwai alamun cewa biyan N30,000 a matsayin sabon mafi karancin albashin ma’aikatan gwamnatin kasar nan ba zai fara a wannan watan ba.

Shugaban kungiyar hadaka ta kula da yarjejeniya tsakanin gwamnati da ma’aikata Abdrafi’u Adeniji shine ya fadawa wakilin jaridar Punch cewa, duk da sanya hannu wanda shugaba Buhari yayi kan dokar mafi karancin akbashin wasu dalilai kan sa fara biyan albashi ba zai iya samuwa a yanzu ba.

Mafi karancin albashi: Kungiyar kwadago tayi gargadi ga gwamnatin tarayya

Mafi karancin albashi: Kungiyar kwadago tayi gargadi ga gwamnatin tarayya
Source: Depositphotos

KU KARANTA:Dalilin da yasa na yafe ma wanda yayiwa diyata fyade

Sakataren wannan kungiya, Alade Lawal shine yayi wannan gargadin ga gwamnatin tarayya da na jihohi akan daura ma kansu nauyin biyan bashi.

A cewar Adeniji, yayinda kungiyarsu ke shirye da tattaunawa akan lamarin, har yanzu gwamnati bata ce komi ba akan tsara jadawalin biyan albashin.

Yace “ Yarjejeniya nada wuya kwarai da gaske. Saboda akwai ababe da dam wadanda yakamata mu duba yayin kullata. Gwamanti zata zanta da kungiyoyi takwas ne a hade wuri guda. Idan har ba’a fara biyan ma’aikata a watan Mayu ba, to abashi zai zame bashi akan gwamnati.

Lawal wanda shine ke tsakanin ma’aikata da kuma gwamnati, yayi gargadi gwamnati akan matsalar dake tattare da rashin kulla yarjejeniya da kungiyar kwadago.

Yayi kira da cewa, a baya da akayi irin wannan yarjejeniya lokacinda aka daga mafi karancin albashin zuwa N18,000 an samu matsala inda ya nuna wannan karo baza a samu irin waccan matsala ba saboda zasuyi abinda zaiyiwa ma’aikatan dadi.

“ A halin yanzu dai gwamnati ta riga da ta sanya hannu akan dokar biyan N30,000 matsayin mafi karancin albashi amma abinda bamu sani ba shine, akwai mataki na ma’aikata daga na 1 zuwa 17 wato level kenan bamu san nawa kowane ma’aikaci zai rika karba ba. Saboda abin na dunkule.

“Mun aika ma gwamnati da wasika ta hanyar ofishin minister kwadago da kuma babban sakataren gwamnatin tarayya domin jin ta bakinsu.” Inji Lawal.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

KU LATSA : Domin karuwa cikin wannan wata mai albarka na Ramadan

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel