Ba abinda ke tsakanina da Sarki Sanusi, inji Ganduje

Ba abinda ke tsakanina da Sarki Sanusi, inji Ganduje

-Gwamna Abdullahi Umar Ganduje yace babu komi tsakaninsa da Sarki kamar yadda wasu jama'a ke ganin cewa ya raba masarautar Sarki Sanusi ne da gayya

-A cewar Gwamnan Sarki Sanusi da shugaban karamar hukuma yakamata a ce yana ganawa bada gwamna ba, bisa ga dokar kundin tsarin mulkin Najeriya

Gwamna Abdullahi Ganduje na jihar Kano ya kare kansa bisa zargin da ake masa na cewa ya kacalcala masarautar Sarki Muhammadu Sanusi na biyu saboda gayya, inda yake cewa sam hakan ba gaskiya bukatar jama’a ya duba wurin yin hakan.

Da yake zantawa da wakilin Daily Nigerian a fadar gwamnatin tarayya dake Abuja, Ganduje yace Sarki ya kamata ya kasance yana kawo rahotone zuwa ga shugaban karamar hukuma amma ba ga gwamna ba.

Ba abinda ke tsakanina da Sarki Sanusi, inji Ganduje

Ganduje da Sarki Sanusi
Source: Twitter

KU KARANTA:Dalilin da yasa na yafe ma wanda yayiwa diyata fyade

Ya kuma yi martini ga masu cewa ya kaskantar da masarautar Kano wacce ta kai shekaru 800 da kafuwa, cewa kawai suna fadin ra’ayin kawunansu ne.

Akan cewar da akeyi ko ramuwar gayyace yayi a kan Sanusi, yace “ A’a ba ramuwar gayya bace, babu komi tsakanina dashi.

“ Alal hakika kamata yayi ya kasance yana kawo rahotonsa zuwa ga shugaban karamar hukuma kamar yadda kudin tsarin mulkin Najeriya ya tanadar. Yayinda shi kuma shugaban karamar hukumar zai tattauna da gwamna kai tsaye.

“ A don haka jama’ar Kano na murna da wannan abu, kuma zamu tabbatar cewa sabbin masauratun zasuyi aiki tukuru domin cigaban jihar Kano.” Kamar yadda Ganduje yace.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

KU LATSA : Domin karuwa cikin wannan wata mai albarka na Ramadan

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel