Shugaban masu rinjaye na majalisar dokoki ya fadi fa'idar kirkiran sabbin masarautu a Kano

Shugaban masu rinjaye na majalisar dokoki ya fadi fa'idar kirkiran sabbin masarautu a Kano

Shugaban masu rinjaye na majalisar dokokin jihar Kano, Baffa Babba ya ce kirkiran sabbin masarautu hudu da gwamnatin jihar tayi zai inganta samar da tsaro a jihar.

A hirar da akayi da Babba a Channels TV a shirin 'State of the Nation' a ranar Juma'a, ya jadada cewa dama masarautun suna nan tun lokacin Jihadin Shehu Usmanu Dan Fadio sai daga baya ne aka rushe su.

Ya kara da cewa an fi samun ingantaccen tsaro a lokacin da akwai masarautun kuma wannan shine dalilin da yasa gwamna Abdullahi Ganduje ya bukaci a farfado da masarautun domin inganta tsaron.

Shugaban masu rinjaye na majalisar dokoki ya fadi fa'idar kirkiran sabbin masarautu a Kano

Shugaban masu rinjaye na majalisar dokoki ya fadi fa'idar kirkiran sabbin masarautu a Kano
Source: Twitter

DUBA WANNAN: An tura 'zauna gari banza' gidan yari saboda taba nonon kwaila

"Sabbin masarautun da aka kafa dama suna nan tun lokacin Jihadi saboda haka ba sabon lamari bane, wasu ne daga baya suka zo suka rushe masarautun kuma sakamakon hakan mun rika fuskantar matsaloli daban-daban.

"A lokacin da akwai masarautun, mun fi samun ingantaccen tsaro. Sarakuna za su san duk wanda ya shigo garin Kano da abinda ya kawo shi garin. Sun kuma san dukkan al'ummar su.

"Amma a yanzu za ka ga mutane suna shigowa garin Kano ba tare da an san ko su wanene ba. Idan aka magance wannan matsalar ba za mu rika samun matsalar baki da za su shigo suna kaiwa mutane hari ba."

Babba ya ce tabarbarewar tsaro a kasar nan yana da nasaba da rashin tsari mai kyau na masarautun gargajiya kuma akwai bukatar a gina shi.

"Rashin bawa masarautun gargajiya kwarin gwiwan gudanar da ayyukansu yadda ya dace ya haifar da matsaloli sosai musamman a fannin tsaro.

"Ya dace a gina masarautun kuma a samar musu da ayyuka da ya dace da su a cikin kudin tsarin mulkin Najeriya musamman a fannin tsaro.

"Karin masarautun da akayi a Kano zai inganta harkar tsaro domin za a bawa sarakuna ikon sa ido a kan yawan shige da fice ba mutane."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku Latsa: Domin karuwa cikin wannan wata mai albarka na Ramadana

Source: Legit

Mailfire view pixel