'Yan siyasa ba su da banbanci da karuwai - Sheikh Gumi

'Yan siyasa ba su da banbanci da karuwai - Sheikh Gumi

Fitaccen malamin addinin Islama mazaunin garin Kaduna, Sheikh Ahmed Gumi, ya ce babu banbanci tsakanin 'yan siyasa da karuwai.

A cewar jaridar Leadership, Gumi ya yi wannan furucin ne yayin da ya ke amsa tambayoyi bayan kammala gabatar da wata lakca a wurin wani taro da Good Shephard Major Seminary suka shirya a Kaduna.

Daya daga cikin mahalarta taron wanda galibin su mazu nazarin addinin kirista ne ya tambayoyi Gumi ko malaman addini musulunci suna da tasiri a kan 'yan siyasa musulmi a Najeriya.

'Yan siyasa ba su da banbanci da karuwai - Sheikh Gumi

'Yan siyasa ba su da banbanci da karuwai - Sheikh Gumi
Source: Twitter

DUBA WANNAN: Hanyoyi 6 da mutum zai kare kansa daga tsananin kishin ruwa a watan Ramadan

A yayin da ya ke bayar da amsa, an ruwaito cewa Gumi ya ce mafi yawancin lokuta 'yan siyasa kan yi kamanceceniya da karuwai shi yasa suke sauya sheka daga jam'iyya zuwa wata jam'iyya.

"Mafi yawancin 'yan siyasa ba su da alkibla shi yasa basa iya zama a jam'iyya guda kuma ba su da banbanci da karuwai," kamar yadda aka ruwaito malamin ya fadi.

A yayin gabatar da kasidarsa, Gumi ya bukaci 'yan Najeriya su kara riko da addinansu da halaye masu kyau musamman a lokacin da harkar tsaro ke kara tabarbarewa a kasar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku Latsa: Domin karuwa cikin wannan wata mai albarka na Ramadana

Source: Legit

Mailfire view pixel