Zamu yi aiki tareda yan sintiri da mafarauta saboda karancin jami’an yan sanda - Kwamishanan yan sanda

Zamu yi aiki tareda yan sintiri da mafarauta saboda karancin jami’an yan sanda - Kwamishanan yan sanda

-Hukumar yan sandan Yobe zasu nemi goyon bayan yan sakai domin yaki da ta'addanci da miyagun laifuka

-A cewar kwamishinan babu wata kasa a duniya dake da yawan yan sanda fiye da jama'arta, don haka neman kwarin guiwa ya zama dole

Kwamishinan yan sandan jihar Yobe, Abdulmaliki Sunmonu yace zasuyi aiki tareda yan sintiri da kuma mafarauta saboda karancin jami’an dake garesu.

Kwamishinan yayi wannan batun ne a ranar Juma’a a Damaturu yayinda yake kaddamar da atisayen “Operation Puff Adder” kamar yadda babban sufeton ‘yan sanda na kasa Mohammed Adamu ya bada umarni.

Zamuyi aiki tare da ‘yan sa kai dalilin karancin jami’an dake garemu, inji kwamishinan yan sanda
Zamuyi aiki tare da ‘yan sa kai dalilin karancin jami’an dake garemu, inji kwamishinan yan sanda
Source: Twitter

KU KARANTA:Dalilin da yasa na yafe ma wanda yayiwa diyata fyade

Sunmonu yace babu kasar dake da wadatattun jami'an yan sanda a don haka amfani da ‘yan sa kai ya zama dole domin kula da al’amuran tsaron al’ummarmu.

“ A yanzu muna zamanin da jama’ar gari ke taimakawa yan sanda ta hanyar yin aiki kamar sune yan sandan. Bambamcin kawai shine horon da jami’an yan sanda ke dashi ya bambanta da na sauran jama’a. Yadda ake gudanar da bincike, kama masu laifuka da kuma mika su gaban shari’a.

“ Mun kaddamar da tsarin hadin guiwa da kungiyoyin ‘yan sakai, PCRC da NURTW duba ga cewa jama’a akwaisu ko ina amma yan sanda ba ko ina suke ba. Babu wurin da zaka samu a duniya inda yan sanda suka fi jama’ar wurin yawa.” A cewar kwamishinan.

Kwamishinan ya bayyana tabbacin cewa atisayen Operation puff adder wanda shugaban hukamar yan sanda ya kaddamar zai taimaka kwarai da gaske wurin yaki da ayyuka marasa kyau, musamman karuwar wadannan ire-iren wadannan miyagun ayyuka bayan kammala zabe zuwa yanzu.

Akan maganar yiwuwan hadin guiwa da hukumar JTF domin gudanar da ayyukansu, kwamishinan yace JTF tana yaki ne da ta’addanci kawai inda kuma Operation puff adder zai hada bangarori daban daban.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

KU LATSA : Domin karuwa cikin wannan wata mai albarka na Ramadan

Source: Legit

Tags:
Online view pixel